Dalilin da ya sa gwamnati ta kwace ginin Otel din Okorocha – Gwamna Uzodinma

0

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya yi karin haske kan kwace wani katafaren Otel din tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha.

Uzodinma ya ce rahoton gwamnatin Emeka Ehedioha ce ta bankado yadda Okorocha ya mallaki wannan gini da karfin tsiya a jihar.

Sannan kuma bayan gwamnati ta kulle wannan Otel sai ya dibi yan iskan gari suka tafi wannan Otek din suka bude shi da karfin tsiya har dan sanda an ji wa rauni.

Uzodinma so ya ke kowa ma ya rika jin tsoron sa – Okorocha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa Gwamna Hope Uzodinma na Imo so ya yi ya bude masa ido shi da magoya bayan sa, domin shi kawai bukatar sa kowa ma ya rika jin tsoron sa.

Okorocha da magoya bayan sa sun yi batacciyar tankiya tsakanin su da hadimin Uzodinma da wasu matasa a ranar Lahadi, a kan kulle otal din matar Okorocha mai suna Royal Spring Palm Hotel da ke Owerri,

Gwamnatin Jihar Imo ta ce an gina otal din bisa karya doka da tsarin gine-gine ta Jihar Imo.

Bayan wannan tankiya da aka yi ce jami’an ‘yan sanda su ka yi awon-gaba da Okorocha, amma daga bisani aka kyale shi ya tafi gida.

An farfasa motoci, kuma an ji wa mutane raunuka. Cikin wadanda aka ji wa raunuka har da dogarin Okorocha, wanda aka yi wa fuskarsa jina-jina sakamakon kafta masa adda da aka yi.

“Ni ban san abin da Gwamnan Imo ke son cimmawa ba. Amma ina jin so ya ke yi shi kawai kowa ma ya rika jin tsoron sa kawai.”

Haka Okorocha ya shaida wa dandazon magoya bayan sa, wadanda su ka je gidan sa a Owerri ranar Litinin domin su na masa goyon baya.

“Ya kirkiro wata baudaddiyar doka ta hanyar samun amincewar ’yan majalisar jihar, dokar da ta ba shi ikon sa a tsare duk wanda ya ga dama. Ina ganin wannan kuwa dabbanci ce kawai.”

Wani hadimin Gwamna Uzodinma mai suna Chinasa Nwaneri, wato Mataimaki Na Musamman Kan Ayyukan Musamman, shi ne ya ja zugar kai wa Uzodinma hari.

Okorocha ya kara shaiada cewa Chinasa da ‘yan jagaliyar da su ka kai masa hari, su samu daurin gindin jami’an ‘yan sanda ne.

“Kuma ‘yan sanda na tsaye su na kallo, ba su yi komai ba, saboda daga Gidan Gwamnati su ke.”

Okorocha ya ce ya na so Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu ya binciki harin da aka kai masa.

Share.

game da Author