Dalilan farfadowar noman auduga a Najeriya

0

Manoman auduga sun bayyana cewa tasiri da darajar auduga ya farfado sakamakon yadda Babban Bankin Najeriya CBN ya hana shigo da yaduka da sauran kayan dinka sutua daga waje.

Manoman sun bayyana cewa sun fara ganin fa’ida da tasirin abin bayan shekaru biyu da haramta shigo da yadukan.

Babban Bankin Najeriya, CBN dai ya hana shigo da yadukan a cikin 2019, domin a farfado da masakun cikin gida da su ka shafe shekara da shekaru a rufe.

Manoman da su ka zanta da PREMIUM TIMES sun ce haramcin shigo da kayan ya taimaka sosai wajen samar da masaku da samar da aikin yi a cikin kasar nan.

Anibe Achimugu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Masu Noman Auduga a Najeriya, ya bayyana wa wakilin mu cewa hana shigo da kayan ya sauya alkiblar harkar noman auduga gaba daya a kasar nan.

“Wannan lamari mu dai ya yi mana dadi matuka, amma bai yi wa masu sumogal din kayayyakin cikin kasar nan ba.”

Ya ce hana shigo da kayan ya zaburar da dimbin manoma su ka karkata ga noma auduga sosai.

“Ai dama idan ka hana shigo da wani abu, to za ka bude kofar samar da shi a cikin kasar ka. don haka sai aka bude kofar manoma su tashi gadan-gadan su noma auduga.

Shi ma wani manomin auduga mai suna Olurunfemi Micheal a Jihar Ekiti, ya ce hana shigo da kayan da masakun mu ke iya sakawa, ya ceci masana’antu ko masakun kasar nan daga durkushewa.

Ra’ayin Zakariyya Adamu, wani manomin auduga a Jihar Kwara, ya yi daidai da ra’ayin Shugaban Kungiyar Manoman Auguga na Kasa.

Shi ma Yahaya Musa daga Jihar Gombe cewa ya yi yanzu noman auduga ya bunkasa, ko’ina aikin saka da hada-hadar auduga ya dawo.

“Hakan ya na nuni da cewa za a rika samun gagarimin aikin yi a harkokin hada-hadar auduga da kuma saka da sauran su.”

A Najeriya dai an fi noma auduga a jihohin Zamfara, Katsina, Borno, Kano, Adamawa da kuma Bauchi.

Shugaban Kungiyar Masu Noman Auduga na Kasa, Micheal, ya ce bashi mai saukin biya da CBN ya bai wa manoman auduga, ya kara bunkasa noman audugar sosai.

“Tare da dalilin lamunin da CBN ta bai wa masu noman auduga, akalla an noma ta kai tan 130,000 a wannan kaka da ake ciki, ko kuma wannan shekarar.”

Haka Adamu ya bayyana tare da jinjinawa ga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sai dai kuma har yanzu masu masakun kasar nan su na kokawa dangane da yadda masu yaduddukan jabu ke dagula masu kasuwancin wanda su ke sakawa.

Shugaban Kungiyar Masu Masaku Na Najeriya, Hamman Ali Kwajafa, ya yi korafi sosai kan masu kwaikwayar kayan da masakun cikin gida su ke sakawa.

“Haka kawai sai ‘yan kasuwa su dauki kwafen irin kayan da masakun mu ke sakawa, su kai kasar Chana a yi masu irin sa.

“Su ke shigo mana da yadudduka ‘wanke-kudin-ka’. Sakawa daya da ka wanke, sai su kode. Kuma su na sayarwa naira 1,000, alhali kuma na mu naira 4,000 ya ke saboda inganci da nagartar sa.”

Daga nan sai ya yi kira da a yi maganin su da gaggawa tare da hana su cin kasuwar da su ke yi sun a gurgunta masu masakun cikin gida.

Share.

game da Author