Wani matashi dake ajin Karshe a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse, ya kashe kansa bayan ya gano budurwarsa ta ci amanar sa ranar Valentine, wato ranar masoya.
Kakakin jami’ar Abdullahi Bello ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shugaban jami’ar ya sa a gaggauta yin bincike akai.
Saurayin mai suna Abdullahi Bashir na mataki na 400 ne a jami’ar kuma yana karatun Lissafi ne. Ya kwankwadi maganin kashe kwari da ake kira Sniper a dakin sa dake makwabtaka da harabar jami’ar.
An tabbatar da rasuwar Bashir ne a asibitin Rasheed Shekoni dake cikin garin Dutse.
Ba ya ga sunan budurwar da aka fadi, wato Rafi’atu ba a bada karin baya ni akan ta ba.