Sa’o’i kadan bayan arcewa da dalibai mata sama a 300 daga makarantar sakandaren mata ta kwana a Jangebe, wani dan cikin garin da aka boye sunan sa, ya shaida wa Gidan Radiyon BBC yadda lamarin marar dadin ji ya faru.
“Ni dan cikin Jangebe ne. Kuma ina tabbatar ma ka cewa ‘yan bindiga sun kewaye makararantar wajen karfe 1:40 na dare.
“Su na zuwa sai su ka kewaye makarantar, su ka harbi maigadi, amma ya tsere, daga nan sai su ka balle kofar shiga makarantar.
“Maharan sun fi su 100. Da su ka shiga, sai su ka fara shiga wani gidan kwanan dalibai, su na cewa “ku tashi lokacin sallah ya yi. Amma su na tashi, sai su ka ga mahara dauke da bindigogi.
“Daga nan sai su ka rika bi cikin kowane gidan kwanan dabilan mata sun a taso su, su na tara su wuri daya. Bayan sun gama tara su, sai su ka rika yin kabbara, su na cewa mun kama ku. Su kuma yaran su na ta kuka.
“Bayan sun tattara su wuri daya, sai da su ka sake bata kusan awa daya da rabi suna harbi a sama. Bayan kamar mintina 20 kuma sai su ci gaba da harbi. Har sai da su ka yi haka kusan awa daya da rabi. Daga nan su ka shiga da yaran cikin daji.”
Wanda ake tattaunawar da shi ya kara da cewa an gano wadanda aka tafi da su din sun kai 374, ta hanyar tattara wadanda su ka rage, ana kiran sunaye a rajistar makarantar.
“Idan an kira dabilba aka ji ba ta amsa ba, to sai a kaddara an yi garkuwa da ita.
“Ina tabbatar maka sai a kira sunan daliba 30, amma shiru babu wadda ta amsa. Sai a ce to an tafi da ita kenan.To ta haka aka nemi dabiba 374 amma ba a gani ba.”
“Daliban makarantar duk mata sun fi 700. Kuma akwai ‘yan jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara, Kano, Katsina da Kebbi da ma wasu jihohin Arewa.’’
Discussion about this post