Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da mummunar tarzomar da ta barke a garin Billiri a jihar Gombe, wadda ta haifar da kone dukiyoyi da masallatan Musulmai.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce shugaban kasa ya roki bangarorin biyu su maida wukaken su a cikin kube, su bari a yi aiki da hankali da tunani wajen warware matsalar.
Wannan tarzoma dai ta barke bayan da wani bangare na Kiristocin garin Billiri su ka ki amincewa da sabon Sarkin da su ka yi zargin shi Gwamna Inuwa Yahaya zai nada masu.
Sunan sarautar dai Mai Tangale, wato Sarkin Kabilun Tangale,
Hasalallun masu zanga-zanga a garin Billiri da kauyukan kewaye da garin sun tare hanyar da ta tashi daga Gombe zuwa Yola, tsawn kwanaki uku.
Sun tare hanyar ce domin nuna fushin su kan bata lokacin da Gwamna Yahaya Inuwa na Gombe ya yi wajen nada sabon basarake mai mukamin Mai Tangale.
Wannan datse hanya da su ka yi ya haifar da matafiya daga Adamawa, Taraba, Benuwai da wasu sassan kasar nan kasa wucewa zuwa wuraren da su ka nufa.
Masu zanga-zanga sun yi zargin cewa Gwamna Inuwa Yahaya na niyyar nada masu wanda ba shi masu zaben sarki su ka zaba ba.
Sun ce Musa Maiyamba ne ya samu kuri’u biyar daga cikin kuri’u tara na masu zaben sarki.
Yayin da Ahmadu Maiyamba da Danladi Maiyamba su ka samu biyu kowanen su.
A kan haka ne su ka yi kira a gaggauta bayyana sunan Musa Maiyamba a matsayin sabon sarki Mai Tangale, domin ya fi sauran yawan kuri’u.
A ranar Juma’a Gwamanatin Gombe ta sa dokar hana fita a Billiri, bayan a masu zanga-zanga su ka kona dukiyoyi da wuraren ibadar Musulmi.
Sannan kuma sanarwar kafa dokar ta hana duk wani taron jama’a a fadin karamar hukumar Billiri.
A kan haka ne Buhari ya nuna tsananin damuwar sa, kuma ya yi kiran a yi aiki da hankali wajen magance rashin fahimtar.
Ya kuma shawarci Musulmi da Kiristoci su zauna lafiya da juna.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ga bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya, inda aka nunu masu zanga-zanga na ragargaa babban masallacin juma’a na garin Billiri, da wasu dukiyoyin da aka ce na musulmai ne.
Haka shugaban Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Bala Lau, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kama dukkan wadanda su ke da hannu wajen kona masallatai da dukiyoyin jama’a a Billiri.