Buhari ya nemi amincewar Sanatoci ya nada Buratai, da wasu hudu Jakadun Najeriya

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sunayen tsoffin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da suka yi murabus majalisad Dattawa domin su amince masa ya nada su jakadun Najeriya a wasu kasashen duniya.

Femi Adesina da ya saka wa wannan takarda hannu ya shaida cewa Buhari ya kuma roki ‘yan majalisan su gaggauta amincewa da sunayen da ya aika domin a nada su fantsama kasashen da za a tura su su fara aiki.

Wadanda aka aika da sunayen su sun hada Janar Abayomi G. Olonisakin (Rtd ), Lt Gen Tukur Y. Buratai (Rtd), Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd), Air Marshal Sadique Abubakar (Rtd), da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (Rtd).

Share.

game da Author