Wasu lauyoyi sun bayyana kwararan dalilai biyar da su ka ce su ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar nada Tsoffin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya jakadun Najeriya a kasashe baban-daban.
Lauyoyin sun ce an nada su Laftanar Janar Tukur Buratai mukaman jakadu ne don kada Kotun Kasa-da-kasa ta Duniya (ICC), ta damke su ta tuhume su da laifukan cin zarafin jama’a da kashe-kashen fararen hula.
Yarjejeniyar Diflomasiyyar Duniya ta 29 ta Taron Vienna Convention dai ta kange tare da haramta kamawa ko tuhumar duk wani jakadan wata kasa a tsakanin kasashen duniya, da nufin tuhumar sa da laifin cin zarafin fararen hula.
Wannan ya sa mutane da dama na ganin cewa Buhari ya yi gaggawar nada su Buratai mukamin jakadun ne don kada a tuhumi zargin kashe-kashen da su ka yi kan talakawa a karkashin mulkin sa.
Dama kuma tun a ranar da su ka sauka jama’a ke ta kiraye-kirayen a gurfanar da su a kotun hukunta laifukan cin zarafin jama’a ta duniya.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Tsoffin Hafsoshin Tsaron Najeriya gata, ya nada su jakadun kasashe daban-daban, mako daya bayan ritayar su.
Wannan gaggawar nadi ta jefa zargi a zukatan jama’a da dama, musamman lauyoyi da a yanzu ke cewa an nada su don a kare su daga tuhumar kotun binciken cin zarafin fararen hula.
Wasu zarge-zargen da ake yi masu, musamman Tukur Buratai, ya hada da kisan-kiyashin ‘yan Shi’a da aka yi a Zariya, cikin watan Disamba, 2015, kisan ‘yan kungiyar IPOB da kuma kisan masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Lagos, cikin 2020.
Gabriel Olonisakin; Tukur Buratai; Ibok Ibas da Abubakar Sadique ne aka nada mukaman jakadun bayan ritayar su.
PDP Ta Nemi ICC da INTERPOL Su Damke Su Buratai A Hukunta Su:
Dama kuma jim kadan bayan ritayar su, jam’iyyar PDP ta yi kira ga Kotun Duniya (ICC) da INTERPOL su gaggauta kama su Buratai su hukunta.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Olagbondiyan ya fitar, ya bayyana cewa su Buratai sun aikata kisan rashin imani da kisan kiyashi a kan araren hula.
Mun Samu Bayanan Da Za Mu Iya Bincikar Buratai –ICC
Cikin shekarar da ta gabata ne Babban Mai Gabatar da Kara na Kotun ICC, Fatou Bensouda, ya yi bayanin cewa sun samu gamsassun bayanan da za su iya bincikar su Buratai kan zargin aikata laifuka a yakin ta’addanci da Boko Haram da Sojojin Najeriya ke kan yi.
Sai dai tun a lokacin Buratai ya ce duk surutai ne, amma lamarin ba ya tsorata shi ko firgita shi.
Sulken Kariyar Bincike Da Buhari Ya Lullube Su Burutai:
Yarjejeniyar Vienna Convention Sashe na 29:
“Duk wani jakadan wata kasa ya haramta wata kasa ta kama shi domin bincike ko gurfanarwa kotu, duk irin laifin da ya aikata. Sulken kariya gare su, ba za a kama su ko hukunta su ba.
“Kada kasar da su ke a zaune ta tura jami’ai a binciki gidajen su ko kwace wasu kadarori ko kayayyakin su.
Afam Osigwe da Inibehe Effiong da wasu lauyoyi da dama, sun cika da mamakin wannan gagarimin laifi da Gwamnatin Buhari ke kokarin binnewa.
Sun yi kira kada Majalisar Dattawa ta amince da nadin mukaman jakadun da Buhari ya nada su Buratai.