Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara wa Sufeto Janar din ƴan sanda Muhammad Adamu wa’adin watanni uku.
Sufeto Adamu ya cika shekaru 35 a aikin gwamnati kamar yadda doka ta gindaya.
A dalilin haka ya sa dole a naɗa sabon sufeton ƴan sanda bayan cikan wa’adin sa a kujerar da ya ke akai.
Ministan Ƴan sanda Muhammad Ɗingyaɗi ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa an kara wa Adamu wa’adin watanni uku ne domin a samu damar zaɓo sabon sufeto cikin kwanciyar hankali.
Akwai manyan jami’an ‘yan sanda 33 da ake ganin a cikin su ne za a nada wanda zai gaji tsohon sufeto janar Adamu: Akwai Sanusi Lemu, Usman Baba, David Folayiwo, Joseph Egbunike da Moses Jitoboh a matakin masu mukamin DIG.
A Matakin AIG kuma akwai Garba Umar, Bello Sadiq, Illiyasu Ahmed, Dibal Yakadi, Zaki Ahmed, HH Karma, Baba Tijjani, Hafiz Inuwa, Lawal Ado, Austin Abonlahor da Isaac Akinmoyede.
Sauran sun hada da Dan Bature, Awuna Donald, Uba Kura, Johnson Kokumo, Zana Ibrahim, Murtala Usman, Maurice Abimbola, Bala Zama, Basen Dapiya, Haruna Mshelia, Aishatu Abubakar, Garba Umar, Aminu Pai, Gwandu Abubakar Omolulu Bishi, Ajani Olasupo da kuma Dasuki Galadanci.
Wani abin mamaki ya faru a Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya a Abuja, a ranar Talata, inda Tsohon Sufeto Janar Mohammed Adamu ya je ofis, sanye da kayan sarki, duk kuwa da cewa ya yi ritaya, saboda ya kai wa’adin shekaru 35 ya na aiki.
Adamu shi da wasu manyan ‘yan sanda sun yi ritaya a ranar Litinin, saboda sun cika ka’idar wa’adin shekaru 35 a aikin dan sanda.
Ya cika shekaru 35 ya na aikin dan sanda, shi da wasu Mataimakan Sufeto Janar su 10.
Wadanda ritayar ta shafa tare da Adamu sun hada da Nkereuwem Akpan, Olafimihan Adeoye, Agunbiade Labore, Undie Adie da Olugbenga Adeyanju.
Sauran sun hada da Asuquo Amba, Mohammad Mustapha, Jonah Jackson, Olushola Babajide da Yunana Babas.
Sai dai kuma duk wadanda aka lissafa din kowa ya ajiye kakin sa ya zauna a gida, amma Adamu ya saka kaki ranar Talata, washegarin ritayar sa, ya je ofis. Wannan abu kuwa ya bai wa ‘yan Najeriya makaki matuka, domin ya karya doka.
Majiya da dama a cikin jami’an ‘yan sanda sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Adamu bai damka ragamar shugabancin ‘yan sanda ga kowa ba, kamar yadda doka ta tanadar.
Baya ga zuwa ofis da ya yi, Adamu na cikin tawagar da ta tarbi Shugaba Muhammadu Buhari a Filin Jirgin Abuja, lokacin da ya koma daga kwanaki hudu da Buharin ya yi a Daura, lokacin da ya tafi sabunta rajistar jam’iyyar APC.
A ranar Laraba a ke sa ran Buhari zai bayyana sunan wanda zai canji Adamu.
Akwai manyan jami’an ‘yan sanda 33 da ake ganin a cikin su ne za a nada wanda zai gaji tsohon sueto janar Adamu: Akwai Sanusi Lemu, Usman Baba, David Folayiwo, Joseph Egbunike da Moses Jitoboh a matakin masu mukamin DIG.
A Matakin AIG kuma akwai Garba Umar, Bello Sadiq, Illiyasu Ahmed, Dibal Yakadi, Zaki Ahmed, HH Karma, Baba Tijjani, Hafiz Inuwa, Lawal Ado, Austin Abonlahor da Isaac Akinmoyede.
Sauran sun hada da Dan Bature, Awuna Donald, Uba Kura, Johnson Kokumo, Zana Ibrahim, Murtala Usman, Maurice Abimbola, Bala Zama, Basen Dapiya, Haruna Mshelia, Aishatu Abubakar, Garba Umar, Aminu Pai, Gwandu Abubakar Omolulu Bishi, Ajani Olasupo da kuma Dasuki Galadanci.