Buhari bai cancanci a kira shi Babban-Kwamandan-Sojojin Najeriya ba – Inji PDP

0

“Idan ya kasance Babban Kwamandan Sojoji ba ya iya shiga gaba kamar yadda Shugaba Buhari yay i alkawarin zai rika yi, sai ya yi zaune turus kullum sai ya dora laifi kasawar sa a kan wasu, to wannan mutumin akwai alamomin tambaya damkam a kan sa.”

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa kasar nan cewa shi talasuru ne, ba jan-gwarzo ba ne. Don haka bai cancanci a kira shi Babban Kwamandan Sojojin Najeriya ba.

PDP ta bayyana haka a bisa dalili da hujjojin cewa Buhari ya yi zaune turus, ya na ganin kasar nan ta kama da wutar matsalolin tsaro ta kowane bangare, amma ya kasa yin wani hobbasa.

“Kasa yi wani katabus da Buhari ya yi wajen dakile mahara da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda, ya kara tabbatar da cewa Buhari kawai burga ce, ba wani jan-gwarzon da za a rika tinkaho da shi ba ne.”

Kakakin PDP Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa kakkausan kalaman wasu sabbin nade-naden da Buhari ya yi ya nuna cewa Buhari kwata-kwata bai ma kamo hanyar magance matsalar tsaro a Najeriya ba.

Cikin wata sanarwa da PDP ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa furucin da Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya ya yi a makon da ya gabata, inda ya ce ko nan da shekaru 20 ba za a iya dakile Boko Haram ba, tamkar burma wa gwamnatin Buhari zurmemiyar wuka ce a ruwan-ciki.

Shi ma Ministan Tsaro Bashir Maganshi, ya bayyana ‘yan Najeriya cewa matsorata ne, su daina tsoron ‘yan bindiga. Kowa ya rika tsayawa ya na kare kan sa.

“To ni ban ga dalilin da jama’a za su rika gudu don ‘yan bindiga sun kai masu hari ba. Kowa ya rika tsayawa kawai. Ya kamata jama’a su rika nuna wa masu garkuwa cewa ko mutanen kauye na da karfin iya tsayawa su kare kan su.” Inji Ministan Tsaro Magashi.

PDP ta kara da cewa wadannan kalamai na raiwa wa talakawa hankali tare kuma da lusarancin da Buhari ke nunawa, su ke kara nuna cewa lallai gwamnatin Buhari ba ta ma kamo hanyar magance wadannan matsaloli ba.

“’Yan Najeriya ba su manta da abin kunyar da ya faru a cikin Najeriya ba, inda Shugaban Chadi Idris Debby ya jagoranci rundunar sojojin kasar, ya fatattaki Boko Haram har cikin Najeriya.

“Idan ya kasance Babban Kwamandan Sojoji ba ya iya shiga gaba kamar yadda Shugaba Buhari ya yi alkawarin zai rika yi, sai ya yi zaune turus kullum sai ya dora laifi kasawar sa a kan wasu, to wannan mutumin akwai alamomin tambaya damkam a kan sa.” Inji PDP a kan Buhari.

Share.

game da Author