Buhari ba ya bukatar rahoton kwamitin Salami kafin ya nada sabon Shugaban EFCC –Fadar Shugaban Kasa

0

Ko da rahoton sakamakon binciken kwamitin Ayo Salami ko babu, to shi Shugaban Kasa ba ya bukatar jira ko bayyana wannan sakamako kafin ya nada sabon Shugaban Hukumar EFCC. Saboda da karfin ikon da dokar kasa ta ba shi ya ke amfani, ba da karfin ikon kwamitin Salami ba, inji Fadar Shugaban Kasa.

Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ne, Garba Shehu ya bayayyana haka a matsayin raddi ga wani rahoton da PREMIUM TIMES ta buga, inda wasu lauyoyi, ciki har da lauyan dakataccen shugaban riko na Hukumar EFCC, Ibrahi Magu, su ka bayyana matukar damuwa, mamaki da al’ajabin yadda Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa, ba tare da bayyana sakamakon binciken kwamitin Salami da aka nada ya binciki zarge-zargen da aka yi wa Magu din ba.

Masu sharhin dai sun nuna cewa kwata-kwata babu mutunci da rashin adalci idan har aka nada madadin Ibrahim Magu ba tare da an bayyana wa duniya laifin da aka kama Magu da shi ba, watanni da yawa bayan kammala bincike.

‘Karfin Ikon Buhari bai jingina ga bangon rahoton Salami ba’ -Shehu

Yayin da wakilin mu ya tuntubi Garba Shehu domin jin ta bakin sa dangane da sharhin da lauyoyi su ka yi cewa Buhari ya yi azarbabin yi wa Magu rashin adalci, sai kakakin na Buhari ya bayyana cewa babu ruwan karfin ikon Buhari da jiran rahoton Salami kafin ya nada sabon shugaban Hukumar EFCC.

“Ya kamata lauyoyin nan su fahimta cewa karfin ikon nada shugaban EFCC da doka ta bai wa Shugaban Kasa, ba shi da wata alaka, nasaba ko kusanci da saurare ko jiran kwamitin Salami. Hanyar jirgi daban, ta mota ma daban. Babu inda su ka hadu ballantana su yi kama da juna.”

Haka Garba Shehuya bayyana a cikin wani sakon da ya aiko wa PREMIU TIMES.

Shehu ya kara da cewa, “doka ce ta bai wa Shugaban Kasa ikon nada shugaban EFCC ko shugaban riko. Kumai ta da ice ta ba shi karfin ikon cire shugaban EFCC. Don haka babu wani abin tsayawa an aka-ce-na-ce a nan.

“Abin da kawai ake bukata bayan Shugaba Buhari ya nada shugaban EFCC, shi ne amincewar Majalisar Dattawa. Kuma ita Buhari ke jira dattawan su amince da wannan nadin.

Dangane da rahoton Salami, Garba Shehu ya ce Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa na nan na aikin fitowa da ‘farar takardar sakamakon binciken kwamitin Salami da kuma matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka a kai.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da lauyan Magu ya bayyana cewa nada Abdulrasheeed Bawa shugabancin EFCC abin tsoro ne matuka.

Lauyan na dakataccen Shugaban EFCC na Riko, Ibrahim Magu, mai suna Tosin Ojaomo, ya bayyana nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Abdulrashim Bawa a EFCC, cewa abin ban-tsoho da mamaki da al’ajabi ne matuka.

Ojaomo ya shiga gidan talbijin na Channels, jim kadan da bayyana sunan Bawa, inda ya yi raga-raga da wannan nadin da Buhari ya yi.

Lauyan wanda ya na cikin lauyoyin da su ka kare Magu a gaban kwamitin bincike na Ayo Salami, ya bayyana cewa akwai tantagaryar rashin adalci da aka nada Bawa ba tare da an bayyana sakamakon binciken da kwamitin Salami ya fitar ba.

‘Gaggawar Nada Bawa’

Ojaomo ya bayyana cewa “abin da kawi kowa ke jira a kasar nan shi ne a bayyana sakamakon binciken Magu, domin a ji laifin da ya yi, idan ma har ya yi laifin. Amma sai aka yi gaggawar nada wanda zai maye gurbin kujerar sa.”

Ya kara da cewa har yanzu babu wani sahihin laifin da aka bayyana wa jama’ar kasar nan, wanda za a kafa hujjar cewa Magu ya aikata. Wannan rashin adalci ne.

Lokacin da Salami ya damka wa Shugaba Buhari sakamakon binciken Magu, ya bayyana cewa akwai takardun jama’a na korafe-korafe har 46 akan sa.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa bayan an damka wa Buhari rahoton binciken, an sake kafa wani kwamiti wanda zai tantance sakamakon binciken.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa, wanda jihar su daya da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda ya yi sanadiyyar korar Magu.

Ta bayyana yadda Ministan Kebbi, Malami ya yi sanadiyyar korar Magu, aka maye gurbin sa da dan Jihar Kebbi.

A yanzu dai ba sabon labari ba ne cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunan Abdulrasheed Bawa, a matsayin wanda ya ke so ya maye gurbin korarren Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Labarin shi ne, wanda aka nada din a yanzu, dan asalin Jihar Kebbi ne, Jihar da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fito.

Dama kuma shi shugaban EFCC tamkar ya na karkashin Ministan Shari’a ne, ba ya gurfanar da gagga da kananan barayin gwamnati sai da shawarar Ministan Shari’a, wanda shi ne Antoni Janar na Tarayyar Najeriya.

Sannan kuma Malami ne ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar korafin zargin cewa Magu na cuwa-cuwa, har ta kai aka damke shi a cikin watan Juli, 2020.

Bayan ya yi kwanaki a tsare, aka sake shi, amma kuma ana kafa masa kwamitin bincike, a karkashin tsohon Cif Jojin Najeriya, Ayo Salami.

Watanni hudu bayan kammala bincike, har yau ba a fito an bayyana tantagaryar laifin da Magu ya yi ba. sannan kuma a asirce a ka yi zaman sauraren binciken na sa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta rika buga laifin zarge-zargen da aka yi wa Magu, ciki har da mallakar kadarori a Dubai.

Sai dai a lokacin da Magu ke karyata zarge-zargen da aka yi masa, shi ma ya zargi ogan sa, Minista Malami da kulle-kullen hada baki da wadanda ake zargi da da sayar da kadarorin da aka kwace a hannun manyan barayi a hanyar da ba ta dace ba.

Sannan kuma ya zargi Malami da hana-ruwa-gudu wajen tadiye wasu bincike da kuma kokarin maido tsohuwar Minsitar Harkokin Man Fetur, Diezani Allison-Maduekwe gida Najeriya, domin a tuhume ta, a hukunta ta.

Bawa dai dan asalin Jihar Kebbi, ne jihar su daya da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda ya yi sanadiyyar sallamar Magu daga aiki.

Bawa: Bawan EFCC Ko Bawan Malami?:

Tilas nada Abdulrasheed Bawa ya haifar da cece-ku-ce a kasar nan, ganin cewa jihar su daya da ogan sa, Ministan Shari’a Abubakar Malami.

Sannan kuma Malami ne sanadiyyar korar wanda aka sauke, Ibrahim Magu bayan sun samu sabani da rashin jituwa a tsakanin su. Har Malami ya rubuta takardar korafi kan Magu ga Shugaba Buhari.

Wannan takarda ta yi sanadiyyar kamawa, kullewa, bincike da korar Magu.

To amma kuma nada dan jiha daya da Malami, zai iya kawo shakku a zukatan jama’a, ko da kuwa babu wani abin da za a yi wa shakku a lamarin.

Yanzu dai ya rage mu ga cewa shin Bawan da Buhari ya nada, bawan EFCC ne ko kuwa bawan Malami zai zama.

Lokaci shi ne alkali kuma shi ne mizani da ma’auni.

Share.

game da Author