Boko Haram sun yi raga-raga da sansanin sojoji, bayan sun kashe soja bakwai a Barno

0

Akalla sojojin Najeriya bakwai ne su ka mutum bayan wani harin bazata da Boko Haram su ka kai wa waninsansanin sojoji.

Sojojin da abin ya shafa sun fito ne daga Bataliyar 153 da ke Marte, Karamar Hukumar da ke cikin Jihar Barno

Wata majiyar cikin sojoji ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram din sun shammaci sojojin ne wajen karfe 10 na safiyar ranar Litinin.

Amma daga baya sun yi karfin halin da su ka kare sansanin, kuma su ka kori Boko Haram din.

Majiya ta ce an shammaci sojojin ne, kuma karfin makaman da Boko Haram din su ka je da su, ya girgiza sojojin matuka.

Bayan ragargaza sansanin sojojin ne kuma sai aka kwashe sojojin da su ka rage daga Marte din aka nausa da su wata karamar hukuma.

Wannan lamari dai ana ganin zai iya sa Marte shiga cikin halin zullumi da barazanar sake afkawar Boko Haram a garin.

Zuwa yanzu dai mahukunta sun bayar da sanarwar cewa sojojin da ke Bangare na 3 a Baga, Cross Kauwa, Kekeno da Monguno da kuma yankunan da ke kewaye da Marte, duk su rika kasancewa cikin shiri.

Majiyar cikin sojojinta bayyana cewa harin da BokoHaram su ka kai a Karamar Hukumar Marten a ranar a Litinin, shi ne na uku accikin wata daya.

Hare-haren baya-bayan nan ya sa dubban mutane tserewa zuwa cikin Maiduguri, babban birnin jihar Barno, wadda tafiya ce ta ysawon kilomita 130.

Kakakin Sojoji Mohammed Yerima dai bai amsa kiran wayar da wakilin PREMIUM TIMES ya yi masa ba. Kuma bai maido amsar sakon tes din da ya aika masa ba.

Share.

game da Author