Boko Haram sun jefa Maiduguri cikin duhu, bayan kai wa hasumiyar wutar lantarki hari

0

Boko Haram sun jefa mazauna garin Maiduguri da kewaye cikin duhu, bayan sun lalata daya daga cikin hasumiyar tashar da ke bai wa garin wutar lantarki daga babbar tashar wutar Najeriya.

Rahotanni sun ce wannan ne karo na biyu accikin watanni uku da irin haka ta faru a Maiduguri.

Rahotanni sun kara da cewa rashin wutar wanda ya shafe mako daya cur, ya jefa mazauna Maiduguri cikin halin kunci.

Wasu mazaunan sun kuma nuna damuwar su ganin yadda aka dauki tsawon wadannan kwanaki ba tare da hukumar da abin ya shafa ta gyara matsalar ba.

“Yanzu fa sati daya kenan cur da Boko Haram su ka kai harin da su ka lalata hasumiyar bada wutar lantarki a Maiduguri.

“Mu na bukatar sanin abin da ya faru da kuma halin da ake ciki a yanzu. Bai kamata mu ci gaba da wannan rayuwar da babu wutar lantarki ba, kuma har yau babu wani bayanin halin da ake ciki.” Inji Ibrahim Abubakar, mazaunin Maiduguri.

Haka wani mai aikin walda, mai suna Moses Bala, ya ce wannan rashin wutar lantarki tsawon mako daya ya durkusar da sana’ar sa ta walda, domin da wutar lantarki ya dogara kadai.

“Ganin yadda aka shafe sama da wata daya ana amfanar wutar lantarki, sai mu ka sakankance, mu ka dogara kacokan da wutar gwamnati. Amma yanzu kuma ga shi an shafe mako daya ba mu da wutar, ballantana mutum ya yi aikin da zai samu kudade.

“Ga shi kuma ni dai ban yi karfin da zan iya sayen janareto ba, saboda ni bako ne a harkar walda.

Haka nan wasu da su ka hada da Musa Idris, Sahabi Abdulrahman, Amina Bello da Talatu Musa duk sun koka a kan yadda wannan rashin wta tsawon sati daya ya gurgunta tare da ruguza masu kananan sana’o’in da su ke dogaro da su.

An tuntubi Manajan Kamfanin Saida Wuta na Adamawa, YEDC, wanda shi ke raba wuta zuwa Adamawa, Barno, Yobe da Taraba, mai suna Kingsley Nkemneme, sai ya ce a tuntubi Hukumar Raba Wuta ta Najeriya, TCN.

Share.

game da Author