BOKO HARAM: Sojoji sun kashe wa Shekau manyan kwamandoji biyu

0

Zaratan sojojin da ke yaki da Boko Haram a karkashin bataliyar ‘Operation Tura Ta Kai Bango’, sun kashe wasu gaggan kwamandojin Boko Haram biyu a ranar Talata.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima ya fitar a ranar Asabar, ta bayyana sunayen wadanda aka kashe da cewa Abul-Bas ne da Ibn Habib, wadanda dama su na cikin wadanda ake nema ruwa-a-jallo.

An kashe su ne a wani gumurzu da sojoji su ka yi da Boko Haram a yankin Pulka, cikin Jihar Barno.

Yerima ya bayyana cewa wannan gagarimin kokarin da sojoji su ka tashi haikan su na kai wa Boko Haram hare-hare a karkashin ‘Operation Lafiya Dole’, ya haifar wa Boko Haram da ISWAP gagarimar asarar manya da kananan ’yan ta’adda a Yankin Arewa maso Gabas.

Ya ci gaba da cewa zaratan a ke karkashin bataliya ta 121 da bataliya ta 151 a ranar Talata sun kai samame kan Boko Haram masu kokarin tsallakawa tsakanin Vuria da Guja, wasu rugage da ke kan hanyar mahadar Banki da Pulka.

Ya ce manyan kwamandojin an kashe su ne tare da wani mayakin su daya a lokacin wannan kwanton bauna da aka yi masu.

Yerima a cikin sanarwar a ya fitar, ya kara da cewa sojoji sun kwace GPMG uku da AK47 bakwai da jigidar harsasai mai albarusai 446, babur samfurin Boxer da wayar hannu, samfurin ITEL 2160 a hannun su.

“Abul-Bas da Ibn Habib na daga cikin manyan kwamandojin da Shekau ke ji da su a Dajin Sambisa da kewaye.

“Abul-Bas babban kwamanda ne, shi ne ma mataimakin Abu Fatima, yayin da shi kuma Ibn Habib, shi ne kwamandan sansanonin Njimia da Parisu da ke cikin Dajin Sambisa,”Inji Yerima.

Share.

game da Author