Mahukuntan Sojojin Najeriya sun karyata wasu rahotannin da su ka nuna cewa Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya har 20, a wata arangamar da su ka yi da zaratan ‘Operation Lafiya Dole.’
Daraktan Hulda Da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima, ya bayyana cewa bayanin kisan da ake cewa an yi wa sojoji 20 karya ce, ba gaskiya ba.
Ya yi bayanin accikin wata takardar da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
Yerima ya ce rahoton wanda aka nuna Hukumar Sojojin Najeriya ta kame bakin ta, ta yi shiru game da kisan sojoji 20, karya ce kawai kuma labari ne na boyi.
Ya kara da cewa wasu ne kawi su ka kirkiri labarin domin su kashe wa fararen hula da sojojin kan su guiwar kara kuzarin dakile Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.
“Kwata-kwata ma babu inda ka kai wa sojojin Najeriya harin da wai har aka kashe soja 20 gaba daya cikin rundunoni da bataliyoyin sojojin da ke yaki da Boko Haram a wurare daban-daban.”
Yerima ya ce harin baya-bayan nan da aka kai wa sojoji masu rakiya da kariya ga masu aikin titi kan hanyar Goniri zuwa Kafa, an yi shi ne tun a ranar 5 Ga Fabrairu, sai kuma na Geidam a ranar 9 Ga Fabrairu, inda sojoji su ka lakada wa Boko Haram kashi raga-raga.
A cewar sa, zaratan ‘Operation TURA TA KAI BANGO’ sun ragargaza Boko Haram, ta yadda a halin yanzu sai gaganiya da fagamniyar neman abinci da magunguna su ke ta yi a wuraren da su ka san akwai karanci jami’an tsaro.
“An ragargaza sansanonin Boko Haram da mabuyar su da dama, sai ta-kai su ke ta yi ba ta-kayan fada ba.”
Daga nan Yerima ya bada bayanin irin gagarimar nasarar kwato manyan makamai da tarwatsa manyan motocin yaki da dama da aka yi wa Boko Haram.
Discussion about this post