BIDIYO: Dakatar Da Kabara: Taron malaman jihar Kano da gwamna Ganduje

0

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da Abduljabbar Kabara daga yin wa’azi a jihar Kano, sannan ta rufe masallacin sa.

Wannan umarni ya biyo bayan zargin tada husuma da yake yi a wa’azin sa.

An sha kai ruwa rana da shi wannan malami game da wasu mas’alolin da ya shafi addinin musulunci in har zargin sa aka yi da kushe wasu sahabban Manzaon Allah SAW.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano Muhammad Garba ya shaida wa manrma labarai cewa gwamnati ta umarci jami’an tsaro su kama duk wani malami da ke wa’azin da zai iya tada zaune tsaye a fadin jihar.

Daga nan sai gwamnati ta ja hankulan malamai da su rika karantar da mabiyan su kamar yadda yake a shari’a.

Share.

game da Author