Bayan kwanaki 10 a tsare, daliban makarantar Kagara sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga

0

Tun da sanyin safiyar Asabar ne’ yan bindiga suka sako daliban makarantar Kagara bayan sun shafe kwanaki 10 suna tsare a hannun su.

Wasu daga cikin mazauna garin Kagara sun tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa tunda sanyi safiyar Asabar aka saki yaran.

An bayyana cewa sai da aka dan yada zango da yaran ofishin ‘yan sanda kafin aka dau hanyar zuwa garin Minna.

Idan ba a manta ba, tun bayan da maharan suka sace diban ake ta kai ruwa rana tsakanin su da gwamnati.

Gwamnatin jihar Neja, karkashin gwamna Abubakar Bello, ta dage cewa ba za ta biya kudin fansa ba don sakin yaran.

Hakan ya yi sanadiyyar dadewar su a tsare, inda har aka samu labarin daga baya maharan sun nemi iyayen yaran su hada wani abi a aika musu su saki ‘yan makarantan.

Share.

game da Author