Bayan fatali da AstraZeneca, Afrika ta Kudu ta tanadi milyoyin rigakafin Pfizer da J&J domin maganin korona

0

Afrika ta Kudu ta fara tanadin milyoyin alluran rigakafi na Pfier da J&J, domin magance kwayoyin cutar korona, bayan da kasar ta dakatar da allurar gwajin rigakafin AstraZeneca, wanda ta ce ba ta magance korona mai saurin kisa, wato Covid-19 ‘varient’.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, bayan da kasar ke ta fafutikar gani yadda za ta shawo kan wannan cuta karo na biyu da ta addabi kasar, mai saurin kisa.

Ramaphosa ya ce Afrika ta Kudu ta tanadi kwalaben allura har milyan 9 zuwa yanzu, yayin da guda 500,000 za su isa kasar nan da makonni hudu, yadda jami’an lafiya za su fara yi wa jama’a allura gadan-gadan.

Ya kara da cewa akwai ma su tulin kwayoyin alluran na Pfizer har guda milyan 20 a kan hanya, saboda a gaggauta dakile wannan sabuwar cutar korona, mai saurin kisa fiye da ta farkon da ta bulla a shekarar 2020.

Kusan mutum milyan 1.5 ne su ka kamu da korona a Afrika ta Kudu, kuma sama da mutum 47,000 su ka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar.

Da farko Afrika ta Kudu ta rumgumi rigakafin korona na AstraZeneca, wanda ke da arha, bai kai na Pfizer da J&J tsada ba.

To sai dai kuma fara gwajin allurar ke da wuya masana kimiyyar kasar su ka gano cewa AstraZeneca ingancin ta bai wuce kashi 22% bisa 100% ba.

Wannan ya sa mahukuntan kasar yin gaggawar fatali da AstraZeneca su ka rungumi Pfier da J&J.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Afrika ta Kudu ta dakatar da rigakafin AstraZeneca, ta ce ba ya maganin korona mai saurin kisa.

Mako daya kadai bayan sama da kwalbar allurar rigakafin korona na AstraZeneca-Oxford ya isa Afrika ta Kudu, mahukuntan kasar sun dakatar da gwajin allurar saboda ta kasa hana wadanda aka yi zakaran-gwajin-dafi da su kamuwa daga rashin lafiya.

Mahukuntan sun ce wadanda aka yi wa gwajin sun kasa samun makaran hana kamuwa daga cutar korona mai zafi, mafi saurin kisa, wato ‘Covid-19 varient’. Ko kuma B.1.351 a takaice.

Ministan Lafiya na Afrika ta Kudu, Zweli Mkhie ya bayyana cewa gwajin allurar rigakafin da aka yi a Jami’ar Witwatersrand ya nuna AstraZeneca cewa ya rage kwayoyin kamuwa da cutar korona da kashi 22% bisa kashi 100% kacal.

“Dalili kenan za mu dakatar da gwajin allurar rigakafin AstraZeneca domin mu sake nazarin tasiri ko rashin tasirin ta a jikin wadanda su ka kamu da cuta bayan an dirka masu wa rigakafin allurar.

“Za mu dakata har sai masana ilmin kimiyya sun ba mu shawarar da za mu dauka a mataki na gaba.” Inji Ministan Lafiyar Afrika ta Kudu, a ranar Lahadi.

Yayin da Afrika ta Kudu ta dakatar da gwajin allurar rigakafin AstraZeneca, ita kuwa Najeriya ta na jiran isowar kwalaben wannan ruwan allurar har guda milyan 16 kafin karshen watan Fabrairu.

Har yanzu dai ba a samu rahoton mutuwar ko da mutum daya daga cikin mutane 2,000 din da aka yi wa gwajin rigakafin korona na ruwan allurar AstraZeneca ba.

Wadanda aka yi wa gwajin dai akasari bas u wuce shekaru 31 ba.

Sai dai kuma kamfanin allurar AstraZeneca ya bayyana a cikin jaridar New York Times cewa gwajin bai yi wa rigakafin adalci ba, domin akasarin wadanda aka yi wa gwajin duk masu shekaru 31 ne ko wadanda ba su wuce ba.

Kenan a ra’ayi ko matsayar kamfanin, yawancin wadanda aka yi wa gwajin ba masu shekaru da yawa ba ne.

Masu wadannan shekaru a cewar kamfanin ba za su zama ma’aunin gamegari na tabbatar da sahihancin AstraZeneca ba.

A Najeriya ma an tabbatar da bullar sabuwar korona mai zafi da saurin kisa, wato Covid-19 varient, ko kuma B.1.351.

Share.

game da Author