Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta jingine umarnin kwace dukkan kadarorin hamshakin attajirin nan Jimoh Ibrahim da AMCON ta yi, bayan hukumar ta zarge shi da kasa biyar bashin naira bilyan 69.4.
Mai Shari’a Okon Abang ya jingine wannan hukuncin kwace wa Jimoh Ibrahim dukkan kadaroin sa, kwanaki bayan da wata kotun tarayya a Lagos a karkashin Rilwan ikawa ta yi fatali da rokon da Jimoh Ibrahim din ya yi na a jingine wancan hukuncin kwace masa kadarori.
Idan ba a manta ba, cikin watan Nuwamba, 2020, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda kotu ta bada umarnin cewa AMCON ta kwace ilahirin kadarorin Jimoh Ibrahim, saboda kasa biyan tulin basussukan da su ka kai naira bilyan 69.4.
Mai Shari’a Abang ya umarci AMCON ta sakar wa Jimoh Ibrahim kadarorin sa, saboda AMCON din ta boye bayanan da ke cikin wasu takardu kafin kotu ta bada iznin kwace kadarorin.
Mai Shari’a ya ce da tun farko AMCON ta gabatar da bayanan ga kotun da ta umarci a kwace kadarorin, to da ba a yi gaggawar kwace su ba tukunna.
Cikin Nuwamba, 2020, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda AMCON ta kwace ilahirin kadarorin Jimoh Ibrahim.
Rahoton ya bayyana yadda Hukumar Kula da Kadarori ta Kasa (AMCON), ta kwace ilahirin kadarori da asusun bankunan da gawurtaccen attajiri, Jimoh Ibrahim ya mallaka.
An rike kadarorin da asusun na sa da na kamfanonin sa saboda kasa biyan bashin naira bilyan 69 da ya yi.
A ranar Laraba ce ta farkon watan Nuwamba, 2020, AMCON ta kwace kadarorin biyo bayan hukuncin da Babban Mai Shari’a na Kotun Tarayya da ke Lagos, Rilwan Aikawa ya yanke a Lagos.
Gaba daya dai an kwace wa Jimoh Ibrahim wanda kuma rikakken dan siyasa ne kadarorin manya, har guda 12.
An kwace gijin NICON Investment Limited, sai NIXON Hotels Limited da ke Abuja, sai kuma NICON Lekki Limited da ke Lagos.
An rike Abuja International Hotels Limited da ke Lagos, an kwace tsohon ginin Allied Bank a Lagos, sai Energy House, NICON Building a Maitama, Abuja, wani gidan sa da ke Victoria Island, Lagos da kuma sai NICON Hotels Building, Lagos.
Har ila yau an kwace katafaren otal din nan na NICON Luxury Hotels, Abuja.
An rike kadarorin ne sakamakon shari’ar da aka maka shi kotu, run 2015, a wata kara mai lamba FHL/L/CL/776/2015.
A ranar Laraba, 4 Ga Nuwamba ne Mai Shari’a Aikawa ya yanke hukuncin kwace kadarorin, tunda ya kasa biyan AMCON naira bilyan 69.
Kakakin AMCON, Jude Nwauzor ya tabbatar da karbe kadarorin. Ya ce an yi amfani da jami’an kotu da jami’an ‘yan sanda.
Ita dai AMCON ta sayi rigimar bashin ne daga hannun Union Bank, amma tun daga lokacin ta bi Jimoh Ibrahim girma da arziki, amma ya kasa biyan kudaden.
Jimoh Ibrahim: Attajirin Da Ya Saba Durkuso Gaban Alkali:
1. Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS), ta taba maka shi kotu, saboda ya kauce wa biyan haraji, tsawon shekaru biyar na naira bilyan 4.86.
An gurfanar da shi a kotu, nasaba da zargin yin amfani da takardun jabu masu nuna Sarifiket na Biyan Haraji, cikin 2012.
EFCC sun maka shi kotu cikin 2012 saboda zargin karkatar da kudade waje.
An sha kara maka shi a nan cikin gida da kuma Amurka.
Kafin buga wannan labarin sai an kasa samun amsa daga kiraye-kiraye da sakonnin tes da aka tura masa.