Ban ce ba kowane dan bindiga ne mai laifi ba – Gwamnan Zamfara

0

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, ya yi karin haske dangane da wani bayani da ya furta a lokacin ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya ce ba a fahimce shi ba.

Matawalle ya je ya sanar da Buhari irin halin da matsalar tsaro a Jihar Zamfara.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan fitowar sa, Matawalle ya ce ba dukkan ’yan bindiga ne masu laifi ba.

Ya bayyana cewa da yawan ’yan bindiga sun dauki makamai ne saboda rashin adalcin da aka rika masu a cikin jama’a.

Bayan jaridu da dama ciki har da PREMIUM TIMES ta buga wannan furuci na sa, daga baya kuma a ranar Laraba sai ya sanar da cewa ba nufin sa ba kowane dan bindiga ne mai laifi ba.

Sanarwar da ta fito daga kakakin yada labarai na Gwamnan Zamfara, Zailani Bappa, Matawalle ya bayyana cewa ba a fahimci abin da ya ce ba ne.

‘Fulani Gwamna Matawalle Ya Ke So Ya Ce, Ba ‘Yan Bindiga Ba’:

Zailani Bappa ya ce kalmar FULANI gwamnan ya so ya ce, ba ‘YAN BINDIGA ba. “Domin ai duk mai hankali babu yadda zai ki kiran dan bindiga mai laifi.”

Don haka mu na kira ga jama’a kada su dauki wancan labari da muhimmanci, domin ba haka ya ke nufi ba.

Abin da gwamna ke so ya fadi shi ne, ‘‘ba kowane BAFULATANI ne ’DAN BINDIGA ba.’’

Share.

game da Author