Ban biya naira bilyan 2 don a kara min wa’adin shekara daya ba – Sufeto Janar Adamu

0

Sufeto Janar na ’Yan Sanda Mohammed Adamu ya karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai su ka buga cewa ya bayar da cin hancin naira bilyan biyu, domin a kara masa wa’adi, bayan ya yi ritaya daga aikin dan sanda.

Adamu ya yi wannan karyatawar a ranar Litinin a cikin wata sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya sa wa hannu kuma ya fitar.

Cikin mokon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa Adamu wa’adin watanni uku, kwanaki uku bayan da ya yi ritaya daga aikin dan sanda.

Kafin lokacin dai wani lauya ya maka Adamu da Buhari kotu, saboda an ga Adamu ya shiga ofishin sa sanye da kayan sarki, kwana daya bayan cikar wa’adin yin ritayar sa.

Ranar 1 Ga Fabrairu, 2021 ce ya kamata ya yi ritaya, domin a ranar ce ya cika shekaru 35 a cikin aikin dan sanda.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa Adamu ya biya cin hancin sama da naira bilyan 2 domin a kara masa wa’adin shekara daya.

Rahoton ya kara da cewa IGP Adamu ya rika bin sarakunan gargajiya neman kamun-kafa, sannan kuma ya rika daukar nauyin wasu masu fada-a-ji su na karakaina Fadar Shugaban Kasa domin a samar masa wa’adin karin shekara daya, amma abin bai yiwu ba.

Sai dai kuma Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bakin kakakin ta Frank Mba, ta ce rahoton karya ce, zubar da kimar shugaban kasa ce, kazafi ne ga Adamu, kuma sakarci ne wanda kotu ka iya gyara wa masu irin wannan karairayin zama.

Share.

game da Author