Kotun Majistare da ke Legas ta bada umarnin a yi wa wata jinjira gwajin gano sahihin wanda ya yi wa jarumar fina-finan cikin da aka haifi yarinya
Mai Shari’a M. O. Tanimola ce ta bada umarnin yin gwajin ga ’yar fitacciyar jarumar mai suna Ronke Odusanya, a ranar Larabar da ta gabata, a Kotu mai lamba 8 da ke kan titin Samuel Ilori, Ogba, Ikeja.
Jarumar mai fitowa a fina-finan Yarabawa ta haihu da wani dadiron ta wanda su ke zaman ‘wa-joko’ tare cikin 2019.
Sai dai kuma mummunan sabani ya shiga tsakanin ta da dadiron na ta mai suna Olanrewaju Saheed, wanda a Legas aka fi sani da Jago.
Wannan sabani ya kai su ga kotu, domin a tilasta wa Saheed daukar nauyin ciyarwa da shayar da jinjirar.
Sai dai kuma wata sabuwa inji ’yan caca, yayin da aka je zaman sauraren shari’a a ranar Larabar da ta gabata, lauyan Saheed ya roki kotu cewa ya na bukatar kotu ta umarci yin gwaajin DNA, domin a gano wanda ya dirka wa Ronke ciki, har ta haihu a cikin 2019.
Lauya ya ce idan kotu ta umarci a yi gwajin, to Saheed zai biya dukkan kudaden da za a kashe wajen yin gwajin, domin gano hakikanin cewa wani farka ne can daban ya dirka wa Ronke ciki, ba shi ba.
Jarumar fim din da lauyan ta sun amince cewa a yi gwajin amma shi Saheed din ya biya kudaden gwaji.
Sannan kuma sun roki kotu cewa ta kula da yadda za a yi gwajin, kuma idan an yi, kotun ce za a damka wa sakamakon gwajin, ba Saheed ba.
Ta memi a yi gwajin a wani boyayyen asibiti a cikin Legas. Kotu ta dage sauraren karar zuwa 31 Ga Maris.
Jaruma Ronke da Saheed sun rabu cikin watan Disamba, 2020, har aka buga labarin cewa sun rabu ne saboda jarumar ta tsiyata shi, har ya kai ga rika sayar da kadarorin sa karkaf, domin kawai ya rika biyan bukatun Ronke, wadda ke tafiyar da rayuwar ta da tsada.