Babban Hafsan Tsaron Kasa, Manjo Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne da har wasu kafafen yada labarai su ka rika watsa labarin cewa sojojin Najeriya sun kara ceto wasu daliban Chibok daga hannun Boko Haram.
Yayin da har yanzu akwai sauran mata 100 a hannun Boko Haram, bayan an karbo wasu daga cikin dalibai mata 270 da Boko Haram su ka yi garkuwa da su tun cikin 2014, cikin makon da ya gabata wasu kafafen yada labarai sun karade kasar nan da labarin sake kubutar wasu daliban daga hannun Boko Haram.
Manyan kafafen yada labarai na duniya, kamar CNN da BBC sun buga labarin, har ma BBC ta ce ta ji ta bakin mahaifin wata daga cikin matan da aka kubutar din, mai suna Halima.
Amma a ranar Lahadi PREMIUM TIMES ta tattauna da sabon Babban Kafsan Hafsashin Tsaron Kasa, Lucky Irabor, har ta tambaye shi ko sojoji sun kwato wasu daliban Chibok daga hannun Boko Haram.
“Abin da mu ka sani dai shi ne sojoji sun matsa wa Boko Haram da farmaki a kowace Karamar Hukumar Jihar Barno, to yanzu haka Boko Haram kowa ta kan sa ya ke yi. Saboda haka daliin wannan farmaki da ake kai masu su na tserewa ne ya bada damar wasu da aka tsare din ke samun sararin guduwa su tsira.”
“Amma dai mu ba mu da wata dalibar Chibok a hannun mu da mu ka ceto daga hannun Boko Haram. To ka ga idan har ba su a hannun mu, to me kuma ka ke so mu tabbatar?
Amma ya kara da cewa fatan su da kokarin duk da su ke yi, shi ne su kwato ko ceto wadannan sauran daibai mata daga hannun Boko Haram.
CNN ta ruwaito mahaifin daya yarinya mai suna Ali Maiyanga ya ce, “wasu daliban sun kara gudowa daga hannun Boko Haram.”
“Da ta kira lambar waya ta da wani layi, sai ta ce, “shin wannan muryar mahaifi na ce na ke ji? Baba kai ne? Daga nan ta barke da kuka, ba ni ma jin abin da ta ke fadi.”
Haka wakilin CNN ya ce mahaifin yarinyar ya shaida masa.
Ya kara shaida wa CNN cewa yanzu haka iyalan sa cike da murna su ke, kuma gidan ya cika da jama’a masu taya su murna.
Kafafen yada labarai na cikin Najeriya sun kasa samun sararin gani ko jin ta bakin Maiyanga, wanda ya ce ya yi magana da Halima ‘yar sa ta lmabar wayar wani jami’in tsaro.
Maiyanga dai an kama masa yara mata biyu, Maryam da Halima, wadda aka ce ita ce ta gudo daga hannun Boko Haram.