Babu wanda yayi rai a hatsarin Jirgin saman Abuja – Rundunar Sojin Saman Najeriya

0

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tabbatar da hatsarin da wani jingin saman ta da ya rikito daga sama a daidai yana kokarin kaiwa ga filin jirgin Abuja yayi ranar Lahadi.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa jirgin ya samu tangarɗa a injin ɗin sa inda ya juyo zai dawo Abuja a hanyarsa ta zuwa Minna.

” Sun kusa isa filin jirgin saman Abuja, sai injin din jirgin ya tsaya, haka suka fado kasa jirgin ya fashe. Babu wanda ya ya rayu cikin sojoji 7 da ke cikin wannan jirgi.

A jawabin da yayi, ministan jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika ya tabbatar da aukuwar hatsarin sannan ya hori mutane su kwanyar da hankalin su zuwa lokacin da rundunar sojin saman Najeriya za ta gama bincike akai.

A karshe yayi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Share.

game da Author