Rajistaran jami’ar Jihar Kaduna Samuel Manshop, ya karyata labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta a yanar gizo cewa wai gwamnatin jihar na shirin canja sunan jami’ar Kaduna zuwa Jami’ar Magajin Garin Zazzau Sambo.
Haka kuma shugaban Jami’ar Muhammad Tanko ya karyata wannan labari inda ya ce labarin kanzon kurege ne kawai ake yadawa.
An rika yada cewa gwamnati zata canja sunan Jami’ar daga jami’ar Jihar Kaduna zuwa jami’ar Magajin Garin Zazzau Sambo a shafukan sada zumunta wanda hukumar makarantar ta karyata.
Wasu masu har sun fara bada shawarar maimakon jami’ar Magajin Garin Zazzau Sambo kamata yayi a canja sunan zuwa jami’ar patrick Yakowa.
Mahukuntar Jami’ar dai sun ce babu wannan magana kwata-kwata karya ce kawai ake yadawa.