Ministan Yaɗa labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ba za ta biya ko sisi ba wajen ceto ɗaliban makarantar Sakandaren Kagara da mahara suka yi garkuwa da su.
Lai Mohammed ya karyata rahoton da ake yaɗa wai gwamnati ta aika wa ƴan bindiga zunzurutun kuɗi har naira miliyan 300 domin su saki ɗaliban makarantar Kagara da malaman da su ka sace.
” Gwamnati ba za ta basu ko sisi ba. Ba zai yiwu ace ana biyan ƴan ta’adda ba saboda haka karya ne ake yi wa gwamnati.
A kan ko ya dace wasu ƴan Najeriya su ziyarci ƴan bindiga domin kira gare su su rungumi zaman lafiya, Ministan ya ce babu wani laifi a hakan.
Ya ce muddin manufar ta yi daidai kuma babbar manufar ita ce zaman lafiya, gwamnati ba ta adawa da duk wani abu da zai kawo da inganta zaman lafiya a kasar nan.
“Bayan yakin, mutane kan zauna don tattaunawa. Don haka idan wasu suka yi kwazon ziyartar waɗannan mutane domin kira gare su su rungumi zaman lafiya, ba na jin cewa hakan bai dace ba.
Ya ce gwamnati na aiki kai tsaye don magance dukkan matsalolin tsaro a kasar nan.
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta samu manya manyan nasarori wajen kau da ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.