Sabon shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya yi alwashin cewa zai yi aiki tukuru wa kasa Najeriya ta yadda, a bayan wa’adin sa, ƴan Najeriya za su hamdala da irin ci gaban da zai kawo hukumar.
Bawa ya bayyana haka da wasu sakonnin ga ƴan Najeriya a lokaci da yake amsa tambayoyin sanatoci a zauren majalisar Dattawa.
Bawa ya shi zai yi tsakanin sa da Allah ta re da bin ka’idojin hukumar da yin amfani da kwarewarsa a lokacin aiki a koda yaushe.
” Zan yi aiki don ya zama dalilin ga shugabannin mu cewa matasa za su iya fafatawa a manyan ma’aikatu kuma su yi nasara.”
Bayyanar Bawa majalisar Dattawa
Bayan amsa tambayoyin Sanataoci 15 da Abdulrasheed Bawa yayi a zauren majalisar dattawa, majalisar ta amince da nadin sa sabon shugaban hukumar EFCC.
Sai da ya dauki Bawa awa biyu cur yana amsa tambayoyin sanatocin kama daga alakar sa da tsoffin shugabannin hukumar zuwa zargin harkallar da ake zaton ya tafka a lokacin da ya ke shugabantar hukumar a jihar Ribas.
Bawa ya ce wadannan zargi basu da tushe. Ya karyata su.
A karshe, majalisar ta amince da nadin sa shugaban hukumar.
Idan ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunan Bawa domin majalisar ta amince da nadin sa sabon shugaban hukumar EFCC makonni biyu da suka gabata.
Bawa shine mai karancin shekaru na farko da aka taba nadawa shugaban hukumar kuma ba dan sanda ba.
Tun farkon soma aukin sa dama a hukumar EFCC din ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a lokacin da Nuhu Ribadu ke shugabantar hukumar.