Jam’iyyar APC ta ce kwata-kwata ba gaskiya ba ne da ake watsa ji-ta-ji-tar cewa wai ta na zawarcin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, domin ya tsaya mata takara a zaben 2023.
Gwamnan Jihar Yobe, kuma Shugaban Riko na Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, shi ne ya furta haka a cikin wata sanarwa da Darakatan Yada Labarai na Gwamna, Mamman Mohammed ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
“Wannan zance da ake yadawa ba gaskiya ba ne, wasu kadai ke watsa zancen na kanzon kurege domin wata bukata kawai. Domin kwata-kwata lokacin fara zancen zaben 2023 bai ba ko kadan. A yanzu mu na da shugaba da ke kan mulki, ko karasa cika shekaru biyu kan mulki bai ma yi ba. Amma wasu sun fito su na zancen 2023.
“Saboda haka mu a yanzu mun maida hankali ne kawai a kan nasarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ke kan samu, daga nan har karshen mulkin sa.” Inji Buni.
Ya ziyarar da wasu gwamnoni su ka kai wa Jonathan, sun je ne kawai domin domin su taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa, a matsayin sa na tsohon shugaban kasa, kuma shugaba ga Najeriya.
Buni ya kara da cewa kuma wannan ziyara ai ba wani abu b ace, domin shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wakilta Jonathan ya wakilci kasar nan a wasu muhimman babutuwa, duk kuwa da bambancin ra’ayi da bambancin siyasar da ke a tsakanin su.
Buni ya ce shi yanzu ya maida hankali ne wajen dinke barakar bambance-bambance da sabanin da ke tsakanin jiga-jigan APC.
“Wannan zance da ake yadawa ba gaskiya ba ne, wasu kadai ke watsa zancen na kanzon kurege domin wata bukata kawai. Domin kwata-kwata lokacin fara zancen zaben 2023 bai ba ko kadan. A yanzu mu na da shugaba da ke kan mulki, ko karasa cika shekaru biyu kan mulki bai ma yi ba. Amma wasu sun fito su na zancen 2023.
“Saboda haka mu a yanzu mun maida hankali ne kawai a kan nasarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ke kan samu, daga nan har karshen mulkin sa.” Inji Buni. a