Gwamnatin Jihar Ogun ta karyata wasu labarai da aka watsa cewa ta gayyato gogarman ta-kifen Yarabawa Sunday Igboho da gungun ta’addancin sa su je jihar su fatattaki Fulani makiyaya.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Ogun, Abdulwaheed Odusile ya karyata rahoton a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i kadan bayan dirar Igboho da tawagar sa Abeokuta, babban birnin jihar.
Sanarwar ta ce rahoton wanda ya fito daga wata tattaunawa da aka yi da mashawarci na musamman ga Gwamna Dapo Abiodun kan yada labarai, ba a fahimci abin da ya ce ba ne kwata-kwata.
“An birkita tare da baddala abinda ya fada kawai don a cimma wata bukata kawai.
Ya ce Hazzan cewa ya yi jihar Ogun za ta hada kai da masu ruwa da tsaki, domin a samu zaman lafiya da tsaro a jihar.
Amma sai aka birkita zancen, aka ce ya ce za a hada kai da Sunday Igboho, amma hakan ba gaskiya ba ne.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Sunday Igboho ya dira Ogun domin fatattakar Fulani daga jihar.
Amma dai wannan jarida ba ta buga labarin cewa an gayyace shi, bisa amsa gayyatar Gwamnatin Jihar Ogun ba.
Sunday Igboho ya dira jihar Ogun domin fatattakar Fulani makiyaya, kwanaki kadan bayan sanarwar da yi cewa daga Oyo zai danna Ogun domin kokar masu Fulani makiyaya a can.
Dan taratsi kuma dan daba Sunday Igboho ya dira jihar Ogun, domin abin da ya kira, ‘ziyarar fatattakar wa jihar Fulani makiyayan da ke cikin ta.
Ya isa jihar bayan tunzira Yarabawa sun kai hare-hare a yankin Ibarapa kan Fulani, tare a banka wa gidan Sarkin Fulanin Oyo wuta.
Yanzu haka dai Sarkin Fulanin da iyalan sa sun yi gudun hijira, sun tsallaka cikin jihar Kwara.
Jim kadan bayan Igboho ya dira jihar Ogun, ya gana da manema labarai, kuma PREMIUM TIMES ta mallaki kwafen bidiyo na tattaunawar da aka yi da shi.
“Mun iso Ogun domin mara wa ‘yan uwan mu baya. Fulani makiyaya na kashe mu a jihohin Yarabawa baki dayan su. Dalili kenan matasa su ka fito domin neman ‘yancin su.”
“Saboda haka na ke cewa dukkan Fulani makiyaya su fice daga Kasar Yarabawa kawai. A yanzu haka an zamu zaman lafiya a yankin Iganga. To ni ba wai a Igangan kadai na ke bukatar a samu zaman laiya ba. Ina jinjina wa Gwamnan Jihar Ogun, saboda ya na kaunar jama’ar sa. Mu ma dalilin zuwan mu Ogun kenan.”
“Za mu je har cikin Yewa, inda Fulani makiyaya ke yi wa mutanen mu ta’addanci nan cikin Jihar Ogun, mu atattake su.” Haka ya furta a cikin bidiyon.
Discussion about this post