Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, ya hakkake cewa ba Fulanin cikin gida ‘yan asalin Najeriya ne ke kashe mutane da garkuwa a cikin dazukan Ondo ba.
Akeredolu ya ce Fulani ne ke yin kisan da garkuwar, amma bakin-haure ne daga wasu kasashe ke shiga su na kaka-gida cikin dazukan jihar.
Gwamnan ya yi wannan bayani a lokacin da Shugaban Hukumar Shige-da-fice mai kula da Shiyya ‘F’, Dora Amahian ta kai masa ziyara.
Ya ce bai yiwuwa a ce wai ba Fulani ne ke masu kashe-kashe ba, ya ce Fulani makiyaya ne, amma masu haurowa daga wasu kasashe, ba wadanda ake tare da su na cikin asalin Najeriya ba shekara da shekaru.
Amahian ya kai wa Akeredolu wannan ziyara ce a ranar Talata, a Gidan Gwamnatin Jihar Ondo, da ke Akure, babban birnain jihar.
“Duk wanda ya ce Fulani ne su ka addabe mu da kashe-kashe da garkuwa da mutane a cikin dazuwakan mu, bai yi laifi ba. Amma dai ba Fulanin asalin cikin Najeriya ba ne. Bakin-haure ne masu tsallakowa daga makautan kasashe.
Amahian ita ke kula da harkokin shige-da-fice a jihohin Oyo, Osun, Ekiti da Ondo.
Daga nan sai Akeredolu ya yi kira da kara kwarin guiwa ga Amahian da ya tabbatar da cewa shi da jami’an ta sun rika sa ido, kada su rika bari bakin-haure na shiga jihohin yankin da nunfin aikata kisa da sata da garkuwa.
“Saboda a gaskiya irin dimbin jama’ar da ke kwararowa a cikin kasar nan a kullum ta kan iyakokin kasar nan abin tayar da hankula ne matukar gaske,
“Duk da na san irin kokarin da ku ke yi domin samar a tsaro a cikin kasa ta hanyar dakile barazana daga makwabtan kasashe, to kuma a gaskiya akwai tayar da hankali da kuma damuwa ainun idan aka yi la’akari da dimbin jama’ar da ke kwararowa a cikin kasar nan daga waje, su shigo cikin dazukan mu su yi zaman-dirshan a cikin Najeriya.
Amahian ta gode wa gwamnan, kuma ta jaddada masa cewa ita da jami’an ta za su kara kwazo matuka.
Discussion about this post