Askarawan korona wanda gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya kafa, sun kama mutane 200 da suka karya dokar Korona wato wadanda basu kiyaye dokokin Korona.
Kwamishinan yada labarai, Garba Muhammed ya shaida cewa Askarawan korona da suka hada da jami’an Korona, ‘yan sanda da duba gari ne suka kama wadannan mutane.
Mutum 102 da aka kama cikin 200 sun biya naira 5000 tara da aka ci su, wasu sai da ya kai ga har an tsare su ne ma a kurkuku.
Garba yace gwamnati ta yi haka ne domin tabbatar da mutanen jihar sun kiyaye dokokin Korona kamar yadda aka gindaya.
” ” Mutane sun yi wa umarnin gwamnati kunnen uwar shegu. Ba su bin dokokin da ka saka don kiyaye kai da kuma yaduwar Korona a jihar Kano. Hakan ya sa dole jami’ai su rika bi suna kama mutane sannan ana cin su tara domin a rika kiyaye wa.
Discussion about this post