APC ta ɗinke a Zamfara, Yari da Marafa sun sasanta cikin Matawalle ya ɗuri ruwa

0

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta dinke tamau yanzu a jihar Zamfara inda bangarori biyu da basu ga maciji suka dinke barakar da ke tsakininsu.

Bangaren tsohon gwamna Abdulaziz Yari, da bangaren Kabiru Marafa su amince su kauda banbanci da rashin jituwar da ya shiga tsakanin su su dawo su haɗa kai.

Shugaban Jam’iyyar APC na rikon ƙwarya, Mala Buni ne ya jagoranci sasantawar inda bayan haka aka naɗa Yari shugaban jam’iyyar a jihar.

” Magoya bayan Marafa da Yari gaba daya sun goyi bayan wannan sulhun kuma sun yi maraba da ci gaban da aka samu na haɗin kan ƴan jam’iyyar, ta yadda za a a iya samun damar wancakalar da gwamnatin matawalle mulki ta dawo hannun APC a jihar.

Gaba ɗaya magoya bayan bangarorin sun amince da sulhun kuma sun lashi takobin za su hada kai su dunkule wuri daya domin ganin Matawalle na jam’iyyar PDP dake mulkin jihar ya ci taliyarsa ta karshe ne a a 2023.

Idan ba a manta ba Tun a lokacin goguwar siyasar 2019, Yari da Marafa suka raba jiha.

Haka ya ɗauko asali ne tun a lokacin da gwamnan jihar a wancan lokaci, wato Yari yayi kakagida a wajen sai dole ya naɗa wanda shi ne ya ke so gwamnan jihar Jigawa.

An yi ta kai ruwa rana a tsakanin bangarorin na su biyu jar ya kaiga jam’iyyar ta kasa gudanar da zabukan fidda ƴan takara na jam’iyyar.

Hakan yayi sanadiyyar rasa duka kujerun takarar Jam’iyyar.

A karshe kuma, Matawalle ya samu kujerar gwamnan daga sama gasassa.

Share.

game da Author