ANA WATA GA WATA: Murar tsuntsaye ta sake bulla a Kano –Daraktan Cututtukan Dabbobi

0

Murar tsuntsaye da ake kira ‘Avian Influenza’ ta sake bulla a Najeriya. Daraktan Kula da Cututtukan Dabbobi, Tsuntsaye da Feshin Maganin Kwari na Ma’aikatar Harkokin Gona da Raya Karkara, Olaniran Alabi ne ya bayyana haka a Abuja.

Wannan cutar ta bulla ne a cikin garken kaji guda biyu na wata gonar kaji a Kano, inda ake kiwon kaji, jimina, agwagwa, kajin Turawa, talo-talo da dawisu a jihar Kano.

Alabi ya yi wannan bayanin a cikin wata takardar sanarwa da aka turo wa PREMIUM TIMES daga Ma’aikatar Harkokin Noma ta Tarayya a ranar Laraba.

Cutar murar tsuntsaye, wadda kuma ake kira da Turanci ‘bird flu’, idan ta bayyana a cikin kaji, ko su nawa ne kashe su ta ke yi baki daya.

Ta kan kama kajin Hausa ko talo-talo da dawisu.

Ana samun cutar a jiki tsuntsaye, musamman kaji, amma ta kan kama mutane jifa-jifa.

Akan dauki cutar daga taba kajin da su ka kamu ko ta hanyar shakar wani ruwa ko miyau ko kashin kajin.

Su ma kaji kan kamu ko da idan aka ajiye su a wurin da aka ajiye kajin da su ka kamu.

Kajin da su ka kamu kan nuna alamun cutar murar ta hanyar zazabi, tari, kumburar makogaro, magaro, matsalar yin numfashi sosai da sauran wasu alamomi.

Wannan cuta ta bulla a Najeriya a karon farko a Afrika cikin 2006.

Sai kuma cikin 2015 ta sake bulla a Kano da Lagos.

Tuni dai aka fara daukar matakai kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Idan ba a manta ba wannan cuta ta yi wa kaji mummunan kisa a cikin 2019, a jihohin Bauchi da wasu jihohi.

Share.

game da Author