An yi wa mutum 4,556 kisan-gilla cikin shekarar 2020 a Najeriya

0

Akalla mutum 4,556 ne aka tabbatar da mutuwar su sanadiyyar hare-haren ta’addanci, ’yan bindiga da sauran rikice-rikice daban-daban a Najeriya a cikin shekarar 2020.

Wata Kungiyar Global Rights Nigeria, mai kare hakkin jama’a ta duniya ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin, inda ta ce jihar Barno ce aka fi kashe jama’a har mutum 1,176, Kaduna, 628; Katsina, 501, Zamfara, 262; sai kuma jihar Nija 254.

Rahoton wanda aka fitar a Abuja a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa mutunen da aka kashe cikin 2020 sun haura wadanda aka kashe a cikin 2019 da adadin mutum 1,368. Domin cikin 2019, mutum 3,188 ne ake da rekod din kashe su aka yi.

Kuuungiyar ta danganta wannan yawaitar mummunan kisan da rigingimu, ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, sai kuma kisan-gillar da jami’an tsaro ke wa farar hula.

“Wannan bala’i ya kara wa ‘yan Najeriya gagarimar matsalar tsaro, a daidai lokacin da korona ta kassara tattalin arziki da rashin aikin yi a cikin kasar.”

“Babban abin damuwar ba wai yawan adadin mutum har 4,556 da ake kashe kadai ne ba, damuwar da abin fargaba shi ne har yanzu gwamnati ta kasa nuna alamar dakile wannan matsalolin da ke haddasa kashe-kashe a cikin kasar.” Inji Global Rights Nigeria.

Babban Daraktan GRN Abiodun Baiyewu, ya hori gwamnatin tarayya ta karfafa tsaro da kuma inganta gwamnati, ta yadda kowa zai zama bai fi karfin ya keta doka ba a hukunta shi ba.

Ya kuma yi kira a kara inganta rayuwar jama’a.

Daga cikin mutum 4,556 da aka kashe a Najeriya cikin 2020, mutum 3,858 fararen hula ne, sai kuma jami’an tsaro su 698.

Cikin wannan jimillar adadi, an kashe mutum 3,720 a Arewa, a Kudu kuma an kashe mutum 828.

Yayin da yawan kisan jama’a da jami’an tsaro a Jihar Barno nacda nasaba da hare-haren Boko Haman da ISWAP, a Jihar Kaduna kuwa akasari hare-hare ne a kudancin Kaduna.

Hare-haren Arewa maso Yamma akasari na ‘yan bindiga ne masu garkuwa da kutane. Sai kuma hare-haren kudancin Kaduna na fadace-fadacen makiyaya da manoma da kashe-kashen ramuwar gayya. A Kaduna an kashe mutum 628, Katsina 501, Zamfara262, Sokoto 99, Kano19, Jigawa 16, sai kuma Kebbi mutum 2.

An kashe mutum 1,508 a Arewa maso Gabas, inda a Borno aka kashe mutum 1,176, Taraba 141, Adamawa 111, Yobe 74, Bauchi 5, sai Gombe mutum 1.

Arewa ta Tsakiya an kashe mutum: 685. Daga ciki, a jihar Neja an kashe 254, Benuwe 145, Plateau 139, Kogi 81, Nasarawa -32 FCT 28, sai Kwara mutum 6.

Wadannan adadin kisa na mutum 4,556 a cikin shekarar 2020, babu adadin wadanda su ka mutu a hadurran mota ko na kwale-kwale a cikin ruwa ko kuma na cututtuka daban-daban, musamman cutar korona.

Share.

game da Author