Ana cutar da mutanen Arewa saboda lalacewa da rashin kishin kan mu da mutanen mu da yankin mu
Har yanzu duniyar arewacin Najeriya ba mu dauka duniyar kudu ta wuce mu a ilimi ba. Mu na yaudarar kan mu da cewa mu na da ilimi, bayan an wuce mu kuma an yi mana nisa, irin nisan sama da kasa. Lallai an yi mana nisa.
Amma har yanzu ba mu gane ba, mu na da’awar komai daga gare mu ya fita. Amma kuma ba haka ba ne.
Addini ya na nan a matsayin sa yadda ya ke. Ci gaban duniya da ilimi su ma su na nan a matsayin su da muhallin su.
Abubuwa biyu ne mabanbanta kuma masu kama da juna, sai dai kowanne ya na zaman kansa ne.
Ilimin tarihi, ilimin falsafa, ilimin sanin halayyar Dan Adam, ilimin ci gaba da na tattalin arziki, ilimin kishin kai, ilimin kare mutunci, ilimin tausayi, ilimin sanin yakamata, da sauran ilimummuka a kan fannoni da dama na rayuwa, an yi mana nisa a kan su nesa ba kusa ba. Shi ya sa a ka fi mu ci gaba.
Mutanen kudu sun yi imani da ilimi, sun amince cewa tarihi shi ne tushen ilimi. Domin ko karatun addini ka yi a karshe za ka ga tarihi shi ne fitilar ka. Sanin tarihi ya zama wajibi a ci gaban rayuwa. Amma mu sani babu wani mutum da ke da cikakke kuma kammalallen tarihi a hannunsa dangane da rayuwa ajiya ko a yau.
Mu na da karancin malaman tarihi saboda karancin malaman yare. Su kuma kalilin din da mu ke da su, ba sa aikinsu yadda yakamata. Ba ma kallon abubuwa yadda su ke, wato kullum mu na dauka cewa mun gane kuma mun kai kololuwar fahimtar inda duniya ta sa gaba, amma fa batun ba haka ya ke ba, gaskiyar magana ita ce ba mu gane ba, kuma ba mu fahimta ba. Me ya sa a ka ce haka shi ne, saboda yadda mu ke rayuwar zaman yan marina kowa da inda ya sa gaban sa.
Dokar kasa ta ba mu damar fadin albarkacin bakin mu amma mun kasa amfani da ita ta hanyar da ta dace. Kullum mu ne sukar juna da aibata juna da ganin illar janun mu a kafafen yada labarai, ta hanyar amfani da yan barandar siyasa, wai duk da sunan amfana da wannan damar fadin albarkacin bakin da a ka ba mu. Kaico!
Akwai abubuwa da yawa da yakamata mu daina kallon su haka su na wuce wa. Saboda yanzu akwai wayewa da ilimi sosai a duniyar da mu ke rayuwa a cikin ta. Sai inda Gizo ke sakar shi ne mu Iyakacin tamu wayewar ta tsaya ne kawai a garuruwan mu, sam ba ma kallon sauran bangarorin duniyar da irin wayewar da su ka samu, don mu koya daga gare su. Shin wai ma, me ya sa za mu tsaya ko yaushe sai wasu sun zo da wani ci gaba sannan mu kwaikwaya? Shin mu ba za mu iya kirkirar abin da wasu za su kwaikwaya daga gare mu ba ne? Ina masu ilimin kimiyyar mu? Ina masana tarihi da sauran fannonin ilimi? Tabbas mu na cikin babban rudani, duhu na dukan duhu. Abin ya zama tamkar irin abin nan na jaki ya koyar da dan uwan sa jaki. Jikin kuma ya ce ya gane, duk kuwa da cewa babu abin da ya fahimta a koyarwar.
Wanda ya san kansa shi ne kuma ya san Ubangjin Sa, wanda bai san kansa ba kuwa, to lallai bai san Ubangjin Sa ba. Abin takaicin shi ne mun kasa bin hanyar da ta dace mu bi don ci gaban yankin mu na arewa, ba mu da aiki kullum sai hauragiya da shirme, matasan mu da yawa sun zama yan shaye shaye, ba sa iya tsinanawa kansu komai ballantana su tsinanawa al’ummar yankinsu da ma kasa wani abin kirki, su kuma manya sun zama gafiya tsira da na bakin ki, in jifa ya wuce kaina kan uwar kowa ma ya fada. Ba mu gane ba, ba mu san ba mu gane ba. Kalli yadda hukumar hisbah ke kallon ‘Black Friday’ a Kano. Shin ‘Black Friday’ kadai hisbah ke kallo a haka?
Shugabanci da a ke yi a yankin mu, irin shugabancin nan ne na mai ido daya a garin makafi. Duk wani rashin ci gaba ya na arewa, mun manta mu ne za mu tashi tsaye mu kawo wa kanmu ci gaba, lokaci ya wuce da za mu zauna zaman jiran wasu su tsara mana yadda za mu yi rayuwa, yin hakan tamkar mu na rusa kanmu ne da kanmu. Mu na dabawa cikinmu wuka da hannayenmu.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu, ya gana da shugaban kasa makonni kadan da suka gabata, ya kuma ba shi kwafin taswirar sake gina birnin na Legas, a dalilin Lalata wasu wurare da wasu tsageru su ka yi a lokacin zanga – zangar ‘#EndSARS’. Kuma tun kafin nan shugaban majalisar wakilai ya ce ba zai sa wa kasafin kudi hannu ba sai an saka diyyar wadanda su ka rasa rayukan su a lokacin zanga – zangar.
Ina gwamnonin Arewan da suka samu matsala a jihohin su? Mun zauna ba neman komai sai wasu da mu ke kallo a matsayin wadanda su ka fi mu wayewa da ilimi sun yi abu sannan ne za mu tashi mu ce lallai mu ma sai mun yi, alhalin mu biyo hanyar da su su ka bi ta bulle da da su ba. Lokacin bayar da tallafin korona sai da Legas ta nemi kudin tallafi sannan mu ka nema. Kuma mutanen mu su ka ce kar a ba mu cinye wa za a yi, su me su ke yi da kudin? Ai ba su kadai ne yan kasa ba.
Gwamnoni su ji tsoron Allah, su sani za fa su sauka daga mulki komai daren dadewa, kuma za su yi kuka da halin da su ka sanya mutane a ciki. Ba tausayi ba tsoron Allah!
Kowa ya na kokarin kawo ci gaba, ku kuma na kawo mana bakin ciki da ci baya. Kullum zalunci a ke yi a kasar nan. Mutane su na shan wahala sosai, rayuwa ta yi wahala. Mutane su na neman taimako ta kowanne hali, kuma sai yan kadan ne su ke tausayawa al’umma. Komai ya na so ya gagari talaka, komai ya yi tsada, komai ninka kudin sa yake yi a kullum. Ba wani babba da ya damu da cewa a na zaluntar mutane, kowa ya na gani. Kowa ya fifita son duniya, shugabanci da kudi a kan komai. An bar bayin Allah su na wahala. Mutane ba ruwan su. kowa a matakinsa dama ya ke nema ya danne mutane. Kowa a sana’ar sa so ya ke ya gallaza wa mutane. Mutane mun zama azzalumai , mu zalunci kan mu, mu zalunci wasu. Abin da Allah ya turo mu duniya kenan mu yi?
Saboda Allah mutanen arewa wane hali ne ba mu shiga ba a yankin mu na rashin ci gaba? Asarar dukiya, asarar rayuka, lalacewar garuruwa, lalacewar gonaki, amma mun kasa magana. Wane gwamna ne mu ka gan shi kamar haka ya je wurin shugaban kasa a fili ya mika masa kwafin sake gina jiharsa.? Garuruwa nawa su ka lalace a arewa sanadiyyar tarzoma? Mutane suna neman abinci an kashe su. Kowa ya ki magana. Wai cewa a ka yi ba su nemi izini ba. Neman halak a arewa ko zuwa gona sai da izini? Duk Najeriya mun fi kowa rayuwa a cikin bala’i da zullumi.
Duk masifar da mu ke ciki a arewa mutanen kudu ba sa cikin irin ta. Sace mutane, kashe kashe, danniya, garkuwa da mutane. rashin hanyayoyi masu kyau, tabarbarewar tattalin arziki, lalacewar aikin gona da sauran su, duk namu ne mu kadai, ba ruwan kowa da mu. Matsalar Arewa tamu ce. Mun kasa sanin kanmu, shuwagabannin mu ba sa kishin mu, mu ma ba ma kishin kanmu, ba ma amfani da ilimin mu da hankalin mu. Mun zama abin da mu ka zama. Sai korafi mu ka iya. Mun kasa kwato wa kanmu yanci . Ba mu da ma su fada aji a malaman addini da siyasa. Kowa ta kansa ya ke babu tausayawa al’umma, sai girman kai da zalunci mu ka iya.
Shekara kusan shida kenan yanzu na wannan mulkin, amma ba mu samu abin da ya kamata mu samu ba. Mu na barci mu na kallon shugaba daga arewa zai gama zango na biyu ba mu amfana da komai ba, sai bakin ciki da nadama. An yi mana ‘raga’ a wancan karon, yanzu ana yi mana daya ragan – ‘raga – raga’ kenan!
Allah Ka ganar da mu, Ka shiryar da mu hanyar Ka madaidaiciya. Allah Ka yaye mana damuwar mu da bakin cikin da ke tare da mu. Allah Ka gyara mana halayen mu Ka kara shiryar da mu.
Muazu Muazu Dan Jarida ne dake karanta labaran turanci a Freedom Radio, Kano
muazumj@gmail.com
08036433199