Kwamitin Ministoci da Gwamnatin Tarayya ta kafa, wanda zai sayar da gidaje da sauran kadarorin da aka kama a hannun barayin gwamnati, sun saka dankara-dankaran gidaje da kadarorin barayin gwamnati a kasuwa, a wurare har 25 daban-daban.
Shugaban Kwamitin Sayar da Kadarorin, Dayo Apata, ya jagoranci tawagar ganin wasu daga cikin gidajen da kadarorin a wurare hudu, bayan ya gana da manema labarai, a ranar Talata a Abuja.
Daga cikin gidajen da manyan kadarorin, akwai gida mai lamba 14, Adzope Crescent, Wuse 2, Abuja, wanda aka kwace a hannun Tsohon Babban Hafsan Tsaro, Alex Badeh.
Gidan ya na daya daga cikin gidajen Badeh da shida da kotu ta kwace a Abuja da wasu wurare.
Apata, wanda ke jagorancin kwamitin, Babban Lauya ne a Ma’aikatar Shari’a. Ya shaida wa manema labarai cewa an bai wa kwamitin sa alhakin sayar da kadarorin, wadanda su ka hada da gidajen maka-makan ilaye, masana’antu, tartsa-tartsan motocin alfarma, kayan amfani da wutar lantarki, kujeru da gadaje da sauran kayan amfani a gidaje.
“Akwai kuma kananan kwale-kwale, kanana da kuma babban jirgin ruwa, sarkokin gwal da sauran kayan
Ya ce har yanzu kwamitin sa na kan karba da lissata kayan da EFCC ta kwace a hannun barayin gwamnati.
Apata ya bukaci duk mai bukatar sayen wani abu daga cikin kadarorin ya duba tallar sanarwar da kwamitin ya yi a cikin jaridun Thisday da Daily Trust, domin ya ga ka’idojin da ake bi kafin a kai ga saye ko sayar da kadarorin.
Wasu Daga Cikin Kadarorin Da Za A Sayar:
The Platinum Residence Exquisite Luxury.
Accommodation, AMSSCO Platinum City, Galadimawa.
No. 6 Ethiope Close Maitama.
No. 6, Ogun River Street, Off Danube Street, Maitama, Abuja.
Plot 1386, Oda Crescent Cadastral Zone A07, Wuse II, Abuja.
No. 19, Kumasi Crescent, Wuse II, Abuja.
No. 14, Adzope Crescent, Off Kumasi Crescent, Wuse II, Abuja.
No. 8A, Embu Street, by Sigma Apartment Wuse II, Abuja.
Platinum Residence Hotel Galadimawa, Abuja.
No. 6, Ogun River Street, Off Danube Street, Maitama, Abuja.
A cikin wannan gidan ne kuma aka tsince dala milyan daya cur, wadda ita ma yanzu haka ta na aljihun gwamnatin tarayya.
Kwamitin Apata Haramtacce Ne –Inji masana
Sai dai kuma wasu masana da dama sun yi korain cewa kwamitin haramtacce ne, domin aikin EFCC ne Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kwace ya bai wa kwamitin.