Hukumar Sojojin Najeriya ta bada sanarwar nada sabon Kakakin Yada Labarai, mai suna Mohammed Yerima.
Sanarwar da aka fitar ta ce Burgediya Mohammed Yarima yanzu shi ne Daraktan Yada Labarai.
Yerima ya canji Sagir Musa ne, wanda shi Musa kuwa ya canji Burgediya Janar Sani Kukasheka ne.
Kafin nadin sa, Yarima ya na da mukamin Mataimakin Darakta ne da ke Hedikwatar Tsaro ta Kasa.
Kafin nadin sa, ya taba zama daraktan yada labarai a Ma’aikatar Tsaro.
Ya shiga aikin soja cikin 1989, kuma ya yi aiki a wurare daban-daban.
Ya na da digiri wanda ya samu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria
Yarima ya taba yin kakakin yada labarai na Runduna ta 81 daga 1995 zuwa 1996.
Sannan kuma ya yi jami’in hulda da jama’a na NDA Kaduna daga 1996 zuwa 2000.
Ya yi kakakin yada labarai na Sojojin Hadin Guiwar Majalisar Dinkin Duniya, daga 2000 zuwa 2002.
Ya yi mataimakin darakta na hulda da jama’a na Ma’aikatar Tsaro, daga 2009 zuwa 2013.
Kafin nadin sa, Yarima ya na da mukamin Mataimakin Darakta ne da ke Hedikwatar Tsaro ta Kasa.
Kafin nadin sa, ya taba zama daraktan yada labarai a Ma’aikatar Tsaro.
Discussion about this post