Wani lauya mai suna Maxwell Okpara, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya a Abuja, inda ya maka Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu gaban shari’a, saboda ya ki sauka daga kan kujerar sa, duk kuwa da cewa ya rigaya ya yi ritaya daga aikin dan sanda tun ranar Litinin da ta gabata.
A karar da ya shigar ranar Laraba, Maxwell ya nemi kotu ta tilasta wa Adamu daina kiran kan sa Sufeto Janar, kuma ya fita daga harkokin da su ka shai ‘yan sanda kwata-kwata.
Cikin kwafen karar, Maxwell ya kuma nemi ita ma kotun ta tilasta wa Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Kasa, PSC ta taka wa Adamu burki.
Maxwell ya nemi kotu ta gaggauta umartar Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wanda zai gaji Adamu a matsayin sabon Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya da gaggawa.
Baya ga Adamu da Hukumar Kula da Aikin Yan Sanda da aka maka kara, Maxwell ya hada da Shugaba Buhari da Ministan Shari’a, Abubakar Malami duk ya maka kotu.
Maxwell ya shigar da kara, bisa hujjar cewa “Dokar Najeriya Sashe na 215 da Sashe na7 NA Dokar Aikin Dan Sanda ta Najeriya, ta shekara ta 2020, ta haramta wa Adamu ci gaba da aikin dan sanda tun daga ranar 1 Ga Fabrairu, 2021.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Sufeto Janar Adamu ya ki sauka kan kujerar sa, duk da ritayar sa.
Wani abin mamaki ya faru a Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya a Abuja, a ranar Talata, inda Tsohon Sufeto Janar Mohammed Adamu ya je ofis, sanye da kayan sarki, duk kuwa da cewa ya yi ritaya, saboda ya kai wa’adin shekaru 35 ya na aiki.
Adamu shi da wasu manyan ‘yan sanda sun yi ritaya a ranar Litinin, saboda sun cika ka’idar wa’adin shekaru 35 a aikin dan sanda.
Ya cika shekaru 35 ya na aikin dan sanda, shi da wasu Mataimakan Sufeto Janar su 10.
Wadanda ritayar ta shafa tare da Adamu sun hada da Nkereuwem Akpan, Olafimihan Adeoye, Agunbiade Labore, Undie Adie da Olugbenga Adeyanju.
Sauran sun hada da Asuquo Amba, Mohammad Mustapha, Jonah Jackson, Olushola Babajide da Yunana Babas.
Sai dai kuma duk wadanda aka lissafa din kowa ya ajiye kakin sa ya zauna a gida, amma Adamu ya saka kaki ranar Talata, washegarin ritayar sa, ya je ofis. Wannan abu kuwa ya bai wa ‘yan Najeriya makaki matuka, domin ya karya doka.
Majiya da dama a cikin jami’an ‘yan sanda sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Adamu bai damka ragamar shugabancin ‘yan sanda ga kowa ba, kamar yadda doka ta tanadar.
Baya ga zuwa ofis da ya yi, Adamu na cikin tawagar da ta tarbi Shugaba Muhammadu Buhari a Filin Jirgin Abuja, lokacin da ya koma daga kwanaki hudu da Buharin ya yi a Daura, lokacin da ya tafi sabunta rajistar jam’iyyar APC.
A ranar Laraba a ke sa ran Buhari zai bayyana sunan wanda zai canji Adamu.
Akwai manyan jami’an ‘yan sanda 33 da ake ganin a cikin su ne za a nada wanda zai gaji tsohon sueto janar Adamu: Akwai Sanusi Lemu, Usman Baba, David Folayiwo, Joseph Egbunike da Moses Jitoboh a matakin masu mukamin DIG.
A Matakin AIG kuma akwai Garba Umar, Bello Sadiq, Illiyasu Ahmed, Dibal Yakadi, Zaki Ahmed, HH Karma, Baba Tijjani, Hafiz Inuwa, Lawal Ado, Austin Abonlahor da Isaac Akinmoyede.
Sauran sun hada da Dan Bature, Awuna Donald, Uba Kura, Johnson Kokumo, Zana Ibrahim, Murtala Usman, Maurice Abimbola, Bala Zama, Basen Dapiya, Haruna Mshelia, Aishatu Abubakar, Garba Umar, Aminu Pai, Gwandu Abubakar Omolulu Bishi, Ajani Olasupo da kuma Dasuki Galadanci.