Kotu a gundumar Bwari dake babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa wani matashi mai suna Adam Abdulrahaman hukuncin zama a kurkuku na tsawon kwanaki 30.
Kotu ta zartar da wannan hukunci ne ne bayan ta kama Abdulrahaman da laifin satan kaji har biyu.
Abdulrahaman ya amsa laifin sa kuma ya roki kotu ta yi masa sassauci.
Alkalin kotun Hassan Aliyu ya bada belin Abdulrahaman akan Naira 5,000.
Aliyu ya ce hukuncin da ya yanke zai zama gargadi ga barayin kajin mutane a Abuja.
Lauyan da ya shigar da karar Tunde Arowolo ya ce Mohammed Salihu dake zama a Action Layout, Bwari, ne ya kai karar satar kaji da ake masa yana neman a taya shi kamo wanda ya ke dauke masa kaji.
Discussion about this post