Allah Sarki Ƴan Arewa, Ana yi mana yadda aka so, shugabannin mu ko a jikin su, Daga Danlami Tamburawa

0

Na kwana cikin bakin ciki tun daga ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi saboda yadda ƴan Ƙabilar Yarabawa ke ci wa mutanen yankin Arewa mutunci ana gani babu wani babba daga yankin Arewa da ya fito ya soki lamarin ko kuma ya ja zugan ƴan Arewa zuwa fadar Buhari domin a ɗau matakin gaggawa.

Wannan kashe-kashe ya tsallake inda rikicin ya samo asali, ya lunkuya har manyan tituna in da matafiya ke jigilar kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu, suna tsame Hausawa suna kashewa, sannan suna banbanka motocin matafiya wuta, kuma ace wai babu wani gwamna ko shugaban majalisa ko kuma wani babban sarki da ya fito ya ce komai akai.

Abinda yake akai shine cin fuskar da kuma kiyayyar sun fito fili karara cewa idan talaka ne ake kashewa shugabannin mu a Arewa ba su fitowa fili su faɗi wa kansu gaskiya ko kuma su shiga wa mutanen su faɗan da ake zaluntar su akai ta hanyar nuna fushin su.

A gaskiya tsakani da Allah, wannan cin mutunci ya wuce misali.

A Arewa ne za ka ga Bayarabe ko Inyamiri da gidajen kansa, filayen kansa, Gonakin kansa, shagunan kansa, sannan har a ayyukan gwamnati za ka ga an basu ayyukan a jihohin da ƴan jihar ma ba a basu ba, amma ba bu irin haka a can yankunan su. Makarantun mu ma haka zaka ga ni, duka jami’o’in dake jihohin Arewa duk sun cika su makil amma kuma a can kyamar ƴan Arewa suke yi. Gwamnonin da shugabannin mu kuma sun yi shiru suna ma ɗaure musu gindi fiye da mutanen su.

Duk ta yadda ka duba za kaga wadanda ba ƴan Arewa ba da ke Arewa na jin daɗin su a yankin Arewa sabanin yadda ake gallaza wa mutanen mu a yankin kudu.

Idan ba a manta ba, a lokacin zanga-zangar EndSars, haka a jihohin Inyamiraiaka rika tattare hanyoyi ana kwashe wa matafiya kayan su. Fulani makiyayi bai tsira ba shi ma a bishi har daji a buge shi a kwashe masa shanu.

Haka ake ta fama amma kuma babu wani da ya fito ya fusata tayi yekuwa ya tunkari fadar Buhari domin a kawo karshen haka ba.

A gaskiya ba zan kammala wannan rubutu ba tare da na jinjina wa gwamnonin jihohin Kaduna da na Bauchi ba wadanda sune gwamnoni biyu a wannan yanki na Arewa da suka fito karara suka nuna bacin ran su da yin kira ga takwarorin su gwamnonin yankin kudu su shiga taitayin su kan yadda ake wulakantawa, cin mutunci da karkashe mutanen Arewa a jihohin su.

Da fatan Allah ya kawo mana saukin wasannan fitintinu, Amin.

Share.

game da Author