Alhamdulillah, Har Yanzu An Kasa Fada Muna Takamammen Laifin Sarki Sanusi, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwa na masu girma, masu daraja, tabbas, ku shaida ne akan cewa, lallai Sarki Muhammadu Sanusi II mutun ne mai tawakkali da cikakken dogaro ga Allah, mutun ne mai juriya, mai hakuri, mai natsuwa, mai hankali, kuma mai hangen nesa. Domin tun lokacin da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yaci mutuncin masarautar Kano, ya tarwatsa ta, ya rusa ta, ya daidaita ta, ya lalata ta, ya wargaza ta, har ta kai matsayin da ba ta da wani tasiri, kuma ya raba kan zuri’ar gidan Dabo, ya haddasa fitina da gaba tsakaninsu da kuma tsakanin Kanawa, ya kacaccala masarautar, kuma ya cire Mai Martaba, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II daga karagar sarautar Kano, Sarki Sanusi ya kame bakin sa, bai taba cewa komai ba akan wannan al’amari, bai taba fadin wata mummunar magana akan kowa ba, saboda imanin sa da kaddarar Allah! Ya mayar da lamarinsa ga Allah, ya natsu, kuma yaci gaba da tafiyar da rayuwarsa, da al’amurransa, kai kace babu abunda ya taba faruwa da shi. Lallai wannan ba karamar baiwa bace da Allah yayi masa!

To amma kamar yadda kuka sani, kuma kuke bibiyar al’amurra, tun a lokacin, shi Gwamna Ganduje bai kyale Sarki Sanusi ba, bai bar shi ba, bai daina fadar maganganu akan sa ba. Kai yanzu ma al’amarin yakai inda yakai, domin an wayi gari a yau, har sai Ganduje ya hada da karya, da soki-burutsu, da sharri, da kage, duk dai saboda ya kare mummunan abun da ya aikata na cire Sarki Sanusi, domin yasan cewa lallai duniya tana nan tana kallon wannan aika-aika da yayi, wadda har abada duniya ba zata taba mantawa da shi ba!

Kamar yadda nasan wasun ku sun kalla, Gwamna Ganduje yayi fira da tashar gidan Talabijin ta Channel, a inda ya sharara karairayi game da wai dalilin da yasa ya cire Sarki Muhammadu Sanusi II, karyar da wallahi ko jahili, kai ko karamin yaro yasan ba gaskiya yake fada ba. Kai bama wannan ba, nayi imani da Allah, shi kansa Gandujen, a lokacin da yake amsa wannan tambaya da dan jarida yayi masa, yana sane da cewa ba gaskiya yake fada ba, kawai dai yana kokarin ya kare kan sa ne ta-ko-halin-kaka!

Jama’ah, har kullun idan ‘yan jarida sun tambayi Gwamna Ganduje, shin mene ne dalilin da yasa ya tabka wannan babbar barna, wannan babbar ta’asa, wannan aika-aika, ta cire mai ilimi da basira irin Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan gadon sarauta. Idan yazo bayar da amsa sai yayi ta kame-kame, yayi ta noke-noke, yayi ta soki-burutsu, kai har an wayi gari yau ya rasa takamammen dalilin ma da zai bayar gamsashshe, da duniya zata yarda da shi. A can baya sun ce dalilin cire Sarki Sanusi shine insubordination (rashin biyayya/rashin da’a/rashin bin doka da sauran su), sannan sun ce rashin zuwa meeting, sun ce yin karan-tsaye ga al’adu, yanzu kuma sai ga shi a firar da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channel, yace wai saboda Sarki Sanusi bai iya hana kan sa zama social critic, ko mai sukar Gwamnati ba.

Shin tambayar da muke son Gwamna Ganduje ya amsa muna ita ce, mu a sanin mu, shin aikin Sarki kam ba yin umurni da kyakkyawan aiki bane da kuma yin hani daga mummunan aiki ba? Idan wannan shine aikin Sarki, to ta yaya za’a yi Sarki Muhammadu Sanusi ya kame bakinsa, yayi shiru, yayi gum, yayi tsit, ya zama hoto, ko ya zama dan kallo, alhali yana gani ana aikata abinda ba daidai ba, ana kokarin cutar da al’ummarsa?

To wai ma Gwamna Ganduje me ya sani game da Sarauta ne, ko kuma abinda ya kamata Sarki yayi, da wanda bai kamata yayi ba? Haba jama’ah! Ko dai saboda mun zama bamu son gaskiya shi yasa ake neman ayi wasa da hankulan mu?

To Alhamdulillah, mu dai mun godewa Allah, da yasa Ganduje da kansa ya fada, kuma duk duniya ta ji, game da irin Sarkin da suke so su samu. Wato Ganduje ya nuna cewa, su sun fi so su samu Sarki wanda yake kamar kurma, wanda ba ya magana, wanda zai yi gum, ya kame bakinsa akan duk abinda ya shafi maslahar al’ummarsa. Ga shi nan kuwa sun dora irin wanda suke so kuma suke bukata. Gashi nan, gwamnati tana ta sayar da kasar Kano da filayen Kano, da wurare muhimmai mallakar al’ummar jihar Kano, wasu filayen kuwa ta mallakawa ‘yan siyasa, magoya bayan ta akan barnar da take tabkawa, amma babu mai kalubalantar su. Sarki Muhammadu Sanusi ne kadai zai iya kallon su, yace sam ba’a yi daidai ba, to su kuwa basa son hakan, shi yasa su ka cire shi, suka dora irin wanda suke so, wanda zai zamar masu dan amshin shata!

Ko akan abun da ya faru kwanannan, na badakalar da ake yi tsakanin Malaman jihar Kano da Abduljabbar, har yanzu babu wata masarautar jihar Kano da tace kala. Har sai da ta kai shi Gwamna Ganduje ne yace, ya kamata Sarki ya sani, a fadarsa fa za’a yi wannan mukabala tsakanin Malamai da Abduljabbar. Ganduje yace shi Dan siyasa ne, saboda haka fadar Sarki ya kamata ta sa baki cikin harkokin addini da al’adun mutane ba shi ba, domin Sarki shine jagoran addini!

Jama’ah kuwa suna ta mayar da martani akan maganar Gwamna, tare da fadin albarkacin bakin su, cewa, Gwamna Ganduje ya manta cewa wannan Sarkin ba zai iya jagorantar al’amari irin wannan ba?

Kai wallahi har ta kai jama’ah suna ta cewa ga fa ranar Sarki Muhammadu Sanusi II nan, suna cewa da shine, da yanzu masarauta ta yi abunda ya kamata akan wannan al’amari na addini da ya shafi al’ummah, kuma yake neman tayar da hankalin al’ummar jihar Kano da ma Najeriya baki daya!

To yanzu dai muna kallo, Ganduje yace dole fadar Sarki ta jagoranci wannan mukabala da za’a yi da malamai da Abduljabbar, duk da dai har yanzu ita fadar bata ce komai ba akan wannan hayaniya. Abun tambayar anan shine, shin masarautar zata amshi wannan abu da Ganduje ya tura masu? Idan kuma sun amsa, shin zasu iya? Kasancewar ba Sarki Muhammadu Sanusi II bane? Yanzu dai duniya ta zuba ido domin ganin yadda wannan al’amari zai kasance.

Sannan maganar masarautar Kano kuma da Gwamna yayi a wannan hira da gidan Talabijin na Channel, ai Ganduje shima yasan karya yake yi, domin babu wata doka da ta kafa masarautar Kano, idan akwai ta kuwa to ya fito da ita. Domin mu dai mun san masarautar Kano tana nan aka kafa Najeriya ma gaba daya balle jihar Kano. Kenan ita masarautar Kano ta girmi Najeriya kuma ta girmi Jihar Kano ma gaba daya, shi yasa a lokacin da masarauta ta fahimci za’a yi mata karan-tsaye shine suka je kotu, wadda Ganduje yake maganar cewa wai Sarki Sanusi yayi karar su. Tun da dai har babu dokar da ta kafa masarautar Kano, to a ina aka samu ikon ayi gyaranta a cikin tsarin mulki? A doka, ba zaka ce zaka gyara abunda babu shi a tsarin dokar ba! Kuma a tsarin mu na dimokradiyyah, ai zuwa kotu ba laifi ba ne ko? Domin misali, ko nine naga cewa Ganduje bai yi man adalci ba, a tsarin dimokradiyyah ina iya zuwa kotu neman ‘yanci na, to kuma balle Sarki Muhammadu Sanusi II!

Kuma mu abun da yake ta bamu mamaki, kuma yake bamu takaici, kuma yake bamu dariya shine, kullun Gwamna Ganduje sai yayi ta yawo, yana yada karairayi, yana cewa, wai ya kirkiro sabbin masarautu ne a jihar Kano saboda ci gaba, wai kuma saboda jama’ah sun nemi ayi hakan! Kuma mu har yanzu, in banda raba kan jama’ah, da cusa gaba da kiyayya, da tarwatsa hadin kai da soyayyar da ke tsakanin zuri’ar Dabo, da rarraba kan mutane, bamu ga wani ci gaba da aka samu a cikin tarwatsa masarautar Kano mai daraja da albarka ba. Idan kuwa har akwai ci gaban da ake da’awar an samu, in ban da sharrin da wannan ya haifar, to sai a kawo muna mu gani!

Kawai abun da duniya ta sani, kuma take akai shine, an kirkiri wadannan masarautu ne domin kawai a bakanta ran Sarki Muhammadu Sanusi II, kuma domin a biya wata mummunar bukata ta hanyar rarraba kan al’ummah!

Kawai don Allah Gwamna Ganduje ya sake lale, ya kamata yayi wani abun da zai amfani kan sa, kuma ya amfani jihar Kano baki daya. Amma don Allah ya kyale Sarki Muhammadu Sanusi II, kamar yadda shima tun da suka cire shi, ya manta da su, yaci gaba da gudanar da al’amurransa, ya zamanto ma da su da rashin su a wurin sa duk daya ne! Domin wallahi, duk karyar da zaku yi, domin ku kare kan ku daga wannan mummunan laifi da kuka tabka, na cire Sarki Sanusi, sam ba zai yi tasiri ba. Domin mutane ba jahilai bane, kuma ba wawaye bane. Suna sane sarai da duk abun da ya faru!

Ta yaya za’a ce wannan bawan Allah, wato Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, har yanzu yana cikin zuciyar ku? Kun kasa kyale shi? Ko da yake kiyayyar da suke yi masa kiyayya ce ta hassada ce. Ita kuwa kiyayyar hassada, sam bata kare wa, muddin wanda ake yiwa hassadar yana nan yana ta ci gaba!

Gwamna Ganduje, a cikin firar sa, ya kawo har da tonon sililin da Sarki Sanusi ya bankado, na wawure dukiyar kasa, a lokacin mulkin shugaba Jonathan. Haba Ganduje, ka sani, ‘yan Najeriya fa ba wawaye bane. Yanzu don Allah waye bai san abun da ya faru ba, na kokarin sace kudin al’ummah? To shike nan so kake yi Sarki Sanusi yayi shiru, kawai don a kyale shi kan mukaminsa, ko kuma don dan wani abu da za’a bashi idan yayi shiru ya lullube wannan sata? Shi fa Sarki Sanusi ba azzalumi bane, kuma sam wallahi ba zai yarda da zalunci ba har abada. Ya kamata kasan wannan!

Kawai mun san cewa kuna hassadar Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II ne saboda Allah Subhanahu wa Ta’ala, cikin iyawarsa da karfin ikon sa, ya sanya shi ya zamanto zakin nahiyar afirka baki daya, kuma abin tinƙahon yammacin ta, gwarzon gwaraza a cikin hidimar al’ummah, wakilin baƙaƙen fata, inuwar talakawa kuma bangon jinginar raunana, gaskiyar da bata taɓa ado da ƙarya ba, fitilar ‘ƴanci a wurin mata da ƙananan yara da masu rauni, dodon azzaluman shugabanni, dodon ‘ƴan danniya, azara’ilun jakadun jari hujja, madubi daga cikin manyan maduban ƙarni na ashirin da ɗaya, kuma ya zamanto waliyi daga cikin waliyan Allah, kuma malami da duk ma’anar malanta suka wanzu a gare shi, kuma mujaddadi, Khalifah Sarki Malam Muhammadu Sanusi II; lu’u-lu’u kuma yakutu a cikin al’ummah. Ina rokon Allah ya ƙara masa imani da nisan kwana, amin.

Kuma wannan baiwa da Allah yayi masa, wadda suke hassadarsa a kan ta, ba fa shine yayi wa kansa ita ba, a’a, wannan duka yin Allah ne, shine yaga dama yayo shi haka!

Kuma wadannan mutane da suka zalunci Sarki Muhammadu Sanusi II, kuma suka zalunci masarautar Kano, sun manta da cewa, tasirin zalunci akan gaskiya al’amari ne na dan wani lokaci. Sun manta da cewa, duk zaluncin mai zalunci wata rana dole za’a wayi gari babu shi, ya wuce, ya zama tarihi, kamar yadda muka gani ya faru da fir’auna da sauran azzaluman shugabanni!

Kamar yadda wani yake fada cewa, a lokacin da aka raka Sarki Muhammadu Sanusi II filin jirgi:

“Yau kuna murna, mu kuma muna kuka, In Shaa Allahu akwai ranar da zaku yi kuka, mu kuma muna shewa muna murna da farin ciki.”

Kuma tabbas, wannan zance haka yake ko shakka babu. Domin duk giyar mulki, da zuga, tare da hassada da ganin kyashi da yake damun wadannan mutane, to dole mun san akwai ranar kin dillaci, akwai ranar da zai zamanto sun sauka daga kan kujerar, wasu su hau, koda kuwa mahaifiyarsu ce mai zartar da kujerar.

• Yalwar Kirjin Sarki Muhammadu Sanusi II

Jama’ah ku sani, lallai yana daga cikin dabi’ar da duk masu son kawo ci gaba da daidaito cikin al’ummah, na jiya da na yau suka yi tarayya akai, wato ‘Jinjinawa mutum akan abinda ya aikata na daidai ko da ya kasance makiyinsu ne, mai nufar su da sharri a koda yaushe’, domin irin wadannan mutanen sun kasance masu faffadar zuciya, wadda take iya ajiye abubuwa a wuraren da suka dace dasu, kuma a lokacin da ya dace.

Babu shakka duk wanda ya waiwaya baya, ya kalli yadda Gwamnatin Ganduje taso ta wulakanta, kuma ta tozarta wannan mashahurin Sarki, sakamakon gaskiya da yake fada masu, akan su gyara kura-kuren da suke tabkawa, ko don kyautata haduwar su da Allah, wanda duk duniya ta shaida cewa, a dalilin haka ne aka nufe shi da cutarwa.

Amma duk da haka, a halin yanzu, wannan bawan Allah, zai iya fitowa ya yabawa Gwamna Ganduje akan wannan abu da ya aikata na kokarin dakile makirci da batanci da zagin da Abduljabbar yake yiwa Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa, da sunan wai yana bai wa Annabi (SAW) kariya, hakika wannan mashahurin Sarki, ya kasance Mukhlisi, kuma mutum mai kokarin ajiye komai a gaskiyar muhallinsa.

Mai yiwuwa wani yayi tsammanin ko Sarki Sanusi yana yabawa Ganduje ne domin samun wata kofa a wurin sa, to mai irin wannan tunani ya sani, wallahi ya makaro, kuma ya kasance wanda bai san waye Sarki Muhammadu Sanusi ba.

Jama’ah ku sani, kawai wallahi tsabagen son Annabi (SAW) da Sahabbansa da dukkanin Ahlul-Bait, shine yasa Sarki Sanusi ya yabawa Gwamna Ganduje, ba wai wani abu ba!

Yanzu ka kalli girman mulki irin na Shugaban Kasa, amma a hakan Sarki Sanusi bai ji tsoro ko shakkar komai ba, ya fito ya kalubalanci Shugaba Jonathan akan wasu kudade da suka bata, ba tare da shakkar me zai je ya dawo ba. Don haka kada kayi tsammanin cewa akwai mukamin wani mai mukami da zai sanya Sarki Sanusi yayi bambadanci ga wani Shugaba, domin ya samu wata kofar shiga a wurin sa!

Daga karshe, ina rokon Allah ya kara dafawa mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, yaci gaba da tsare muna shi, daga sharrin masharranta, ya kare muna shi daga makircin masu makirci, amin.

Sai mun hadu a rubutu na gaba in Allah yaso. Nagode.

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam ta lambar waya kamar haka: 08038289761

Share.

game da Author