Aikin titin jirgin kasa ya tsaya saboda ma’aikata 60 sun kamu da cutar korona – Amaechi

0

Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa aikin karashen titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan ya tsaya ne saboda wasu daga cikin ma’aikatan sun kamu da cutar korona a cikin watan Janairu da ya gabata.

Amaechi ya bayyana cewa amma gwamnatin tarayya ta fadada ko ta kara tsawon titin zuwa Abute Meta zuwa bakin tashoshin ruwan Lagos.

Ministan ya yi wannan karin haske a lokacin ziyarar duba-garin manyan tashoshi uku da kananan tashoshi bakwai da aka gina a cikin jihar Jihar Oyo.

Ya ce kamfanin CCECC masu yin wannan kwangila sun hada wannan layin dogo da tashar ruwa ta Lagos.

“Ba zan iya cewa ga lokacin da za a bude aikin ba, amma dai da farko an aza kammalawa a budewa cikin watan Janairu, 2021, to sai aka daga, saboda wasu daga cikin ma’aikatan sun kamu da cutar korona.’’

“Cikin watan Janairu da ya gabata, sama da ma’aikatan titin jirgin kasa 60 ne su ka kamu da cutar korona. Wannan ya sa aka samu tsaikon da ya hana a kammala aikin a cikin watan Janairu.

“Amma a yanzu na lura kusan dukkan kanana tashoshin ana matakin karshe na kammala aikin su. Yannzu haka har ma an kammala daura na’urorin sanyaya dakuna.

“wadanda su ka take wa Amaechi baya sun hada da Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar Sufuri, Magadalene Ajani, Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Kasa, Musa Al-Hassan da Babban Daraktan Hukumar Jiragen Kasa, Fidet Okhiria.

Bayan sun isa Lagos, Amaechi da ‘yan tawagar sa sun shiga jirgin kasa zuwa tashar jiragen ruwa ta Apapa, domin tabbatar da cewa an kammala aikin titin mai isa har bakin tashar jiragen ruwa.

A tashar Apapa, Amaechi ya yi kakkausan gargadin cewa direbobin manyan motoci su daina ajiye motocin su bakin titin jirgin kasa.

Ya ce nisan titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan, killomita 157 ne.

Share.

game da Author