Tun bayan damke tsohon hadimin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakasai na ke ta bibiyan shafukan sada zumunta a yanar gizo domin karanta ra’ayoyin jama’a game da damke sa da SSS suka yi.
Duk da cewa hukumar SSS ta fito ranar lahadi, inda ta tabbatar da haka, da dama cikin mutane sun nuna rashin jin dadin su kama Salihu da aka yi sai dai kuma allura ce ta hako garma.
A nawa ra’ayin ban ga dalilin da zai sa mutumin da ke aiki karkashin wata gwamnatin da bai yi na’am da salon mulkinta ba ya ci gaba da aiki karkashinta ba.
Idan kana yi, kana yi, idan baka yi kawai baka yi. Duk wanda ya fito ya za gi Buhari a Kano cikin ma’aikacin gwamnatin Kano ya ci amanar Ganduje. A matsayin hadimin Ganduje, dole ya iya wa bakin sa da kuma ra’ayoyinsa. Idan yana so ya fito fili ne sai ya yi sallama da aikin sa ya koma fagen yin adawa da gwamnatin Buhari.
Duk kalaman da za ka yi a kujerar da kake akai, za a jingina shi da wannan ra’ayin gwamnatin da kake wa aiki ne.
Saboda haka shawara ta ga masu aiki tare da manyan ‘yan siyasa shine, idan za su yi magana su tuna cewa suna aiki karkashin wani ne da dole su kare shi sannan su iya bakunansu ga duk wani abu da zai zamo musu na cin mutunci ne. Domin ba zai tsaya ga su ba kawai zai shafi har wanda suke yi wa aiki.
Annabi Sallalahu alaihi wasallam ya ce ” Wanda yayi imani da Allah da ranar Lahir, Ya fadi Alkhairi ko yayi Shiru.” Idan shawara ce kana kujerar irin haka sai ka garzaya kai da shi ka bada shawarar ko amma ka fito karara ka ci wa gwamnatin da kake kai kana holewar ka a dalilin ta bai dace ba.
A rika kula.
Discussion about this post