Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa akwai matukar bukatar gaggauta bunkasa abinci a Najeriya, idan aka yi duba da irin yadda ake samun karin yawan haihuwa birjik a kasar nan.
Osinbajo yace maganar gaskiya yawan jama’ar kasar nan ya tsere wa karfin tattalin arzkin kasar nan fintinkau.
“Akwai bukatar Najeriya ta gaggauta samar da tsarin bunkasa abinci da gaggawa, saboda maganar gaskiya yawan jama’ar kasar nan ya zarce karfin tattalin arzikin cikin kasa nesa ba kusa ba.
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa talauci da kuncin rayuwa da fatara sun karu sosai a kasar nan sakamakon barkewar cutar korona, wadda ta janyo komai ya tsaya cak, tsawon watanni da dama.
Osinbajo ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Hanyoyin Bunkasa Abinci da Majalisar Dinkn Duniya ta shirya (UNFSS), wanda aka gudanar ta intanet da talbijin da mahalarta sama da 700 su ka halarta, amma kowa daga gida ko ofis.
An shirya taron ne domin gano tsari da kalubalen bunkasa harkokin noma a Najeriya, ta yadda kasar nan za ta bunkasa sosai nan da shekarar 20230, a fannin wadata da yalwar kayan abinci.
“Rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin cin abinci mai rai da lafiya, barazana ce ga kiwon lafiya daga wannan karni zuwa wani karnin.”
Ya ce babu yadda za a yi abinci garau-garau ya iya rike mutum har ya inganta lafiyar sa a irin halin kunci da fatarar da kasar nan ke ciki.
Ya ce idan ana so a wadata al’ummar kasar nan da wadataccen abinci, to tilas sai an tashi tsaye, ta hanyar zamanantar da harkar noma da kuma samo dabarun hana manoma dibga asara a lokacin da su ka girbe amfanin gonar su.
“Ya kamata kuma a ce shi kan sa abincin da mu ke ci, ba mai gurbata yanayi ba ne. Ya kamata ya kasance mai bunkasa yanayi ne matuka.”
Cikin wadanda su ka yi jawabai a wurin taron, akwai Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed da masana harkokin abinci mai rai da lafiya da dama.