Abin da ya sa za mu gina titin jirgin kasa dodar daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana fa’idar da ya ce ke tattare da gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ta Jamhuriyar Nijar.

Da ya ke kaddamar da aikin titin daga ofishin sa, Buhari ya bayyana cewa idan aka kafa titin, zai samar da makudan kudaden shiga ga kasar nan tare da samar da aikin yi sosai.

Ya kara da cewa al’ummar Nijar a na su bangaren a su samu saukin zirga-zirga zuwa cikin Najeriya.

Haka Buhari ya bayyana a lokacin da ya ke kaddamar da aikin a ranar Talata a ofishin sa, ta hanyar ‘zoom’.

A ta bakin sa, aikin ginin titin jirgin zai ci dala bilyan 1.96. Zai kasance hanya ko kuma mashiga da maitar da kayan kasuwanci daga Najeriya zuwa kasashen Afrika. Kuma daga wadannan kasashe zuwa cikin Najeriya ta hanyoyin tashoshi.

“Idan aka kammala wannan gagarimin aiki, ai zama hanyar fitar da kaya daga jamhuriyar Nijar da sauran kasashe.

Najeriya kuma za ta samu makudan kudaden shiga ta hanyar fadada kasuwanci da cinikayya a tsakanin kasashen. Tare kuma da saukaka zirga-zirga.” Inji Buhari.

Titin jirgin dai zai tashi daga Kano, wadda can ne cibiyar kasuwancin Arewa, zai bi ta Kazaure, Daura, Katsina, har zuwa Jibiya daga can ya zarce Jamhuriyar Nijar a garin Maradi.

Maradi dai ba ta da nisa da Jibiya, daya daga cikin kananan hukumomin Jihar Katsina.

Sai dai kuma wakilin mu ya fahimci cewa da yawa mutane a Kano ba su cika murna da wannan kaddamar da titin jirgin kasa ba.

Ya yi da wani mai suna Halliru Sani ke ganin abin duk “tatsuniya zai zama kamar tashar lantarkin Mambilla”, shi kuwa Lamido Isma’il cewa ya yi, “a gaskiya mu a Kano mun fi murna idan aka yi mana titin jirgin da aka yi alkawari shekaru uku da su ka gabata daga Ibadan zuwa Kano.

“Amma shikenan mu kullum sai dai a ce an kaddamar da abu, amma shiru ka ke ji. Nan a cikin watan Janairu na ga jaridar ku ta buga cewa gwamnatin Buhari ba ta da kudin da za ta yi aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano. To ina ta samu na aikin titin zuwa Nijar? Ko shi ma duk bagararwa ce kawai?”

Da yawa na ganin cewa Kanawa sun fi bukatar titinjirgin kasa zuwa Lagos, ba Kano zuwa Nijar ba.

Share.

game da Author