Abdulrasheed Bawa, sabon shugaban hukumar EFCC

0

Abdulrasheed Bawa dan asalin jihar Kebbi ne kuma shekarunsa 40 daidai a duniya.

Bawa yayi karatu a jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto inda daga nan sai ya fada aikin EFCC wanda shugaban hukumar na farko Mal Nuhu Ribadu ya dauke shi aiki.

Tun daga wancan lokaci ya ke aiki a hukumar har ya kai ga wannan matsayi.

A shekarar 2015, an nada Bawa ya jagoranci bincikes harkallar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Allison-Madueke.

Idan har majalisar Dattawa ta amince da nadin Bawa, zai zama mutum na farko da ya dare kujerar shugabancin EFCC ba tare da yana da alaka da aikin dan sanda ba. Duk sauran yan sanda ne a baya tun daga wanda aya kafa hukumar, wato Malam Nuhu Rinadu har zuwa Ibrahim Magu wanda har yayi ya gama majalisar Dattawa bata amince da nadin sa ba.

Bawa ne yake kula da ofishin hukumar dake Legas har zuwa yanzu da aka nada shi shugaban EFCC.
Sannan kuma a tsaon aikin sa a hukumar EFCC tun daga 2004 zuwa yanzu ya jagoranci manya-manya bincike da kwato makudan kudade da aka yi awon gaba da su a kasar nan ciki har binciken harkallar Atlantic Energy a kasheshen UK, Najeriya, UAE da Canada.

Sannan kuma shine akan gaba wajen binciken harkallar sama da fadi da tsohon gwamnan Neja yayi wanda hukumar ke bincike.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce majalisar za ta tantance Abdulrasheed Bawa a zauren majalisar kamar yadda ta saba yi a baya.

Lawan ya fadi haka a zauren majalisa ranar Talata da ya ke karanta wasikar shugaban Kasa Buhari na bukatar majalisar ta amince da nadin Bawa shugaban hukumar EFCC.

Share.

game da Author