Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar cewa jami’an ta sun ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su, sun kwato shannu 11 da wasu motoci da aka sato daga kananan hukumomin Kaura Namoda, Birnin-Magaji da Gusau.
Kakakin rundunar ƴan sandan Muhammad Shehu ya sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai a Gusau.
“A ranar 4 ga Faburairu rundunar Operation Puff Adder sun ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a bayan makarantar sakandaren Namoda da Zangon Danbade a karamar hukumar Kaura Namoda.
“A ranar 3 ga Faburairu rundunar Puff Adder dake aiki a kasuwa a Nasarawa Godal a karamar hukumar Birnin Magaji sun kama shannu 11 da barayi suka sato a karamar hukumar Maradun.
“A
Sannan ranar 6 ga Faburairu wata Hajiya Zainab Saidu dake zaune a Gidan Dawa Gusau ta kawo kara a ofishin ‘yan sandan dake Tudun Wada cewa barayi sun sace mata mota.
“Nan da nan jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike inda suka tsinci motar a hanyar Premier dake Gusau.
Shehu ya ce rundunar ta ci gaba da gudanar da bincike domin kamo barayin da suka aikata haka a jihar.
Discussion about this post