Sakatariyar yaɗa labaran gwamna Abubakar Bello na jihar Neja, Mary Noel-Berje ta bayyana wa manema labarai a garin Minna cewa mahara sun saki fasinjojin NSTA da suka yi garkuwa da su.
Idan ba a manta a cikin makon jiya ne mahara suka sace fasinjojin motar NSTA a hanyar Zungeru zuwa Minna.
Maharan sun yi ikirarin ba za su saki fasinjojin ba sai gwamnati ta biya su kudin fansa har naira miliyan 500 kafin su sake su.
A wani bidiyo da suka fitar maharan sun rika nuna karfin makaman su suna yi wa gwamnati izgilanci da yi musu kuri cewa ba za su saki fasinjojin ba.