Ƙungiya ta raba wa Zawarawa 120 tallafin naira miliyan 10 a Abuja

0

Ƙungiya mai zaman kanta ta raba wa Zawarawa 120 tallafin naira miliyan 10 a Abuja.

Shugaban ƙungiyar Offiong Anyanwu ya sanar da haka a Abuja a makon jiya.

Anyanwu ya ce an kafa wannan kungiya ce domin a inganta rayuwar gajiyayyu, talakawa, Zawarawa da yara marayu.

“Kungiyar nan kan biya kuɗaɗen makarantar yara marayu da dama domjn suma su sami ilimi kamar kowa.

“Sannan akan horas da mata sana’o’in hannu domin samun wani aiki ko sana’ar da za su iya ciyar da kansu da ‘ya’yan su.

Bayan haka ya kara da cewa Kungiyar ta rabawa Zawarawa da gajiyayyu abinci da sauran kayan masarufi a Abuja. Sannan kuma ya ce an ba kowacce mace jalin naira 50,000 ta fara sana’a.

Anyanwu ya ce kungiyar ta horas da mata sana’o’in hannu kamar su yin sabulu, man shafawa da sauransu domin suma su fara cin gashin kansu.

Share.

game da Author