Jimlar kananan sojoji har 127 ne su ka shirya ajiye kaki kwanan nan, duk kuwa da gagarimar matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta a sassa daban-daban na kasar nan.
Sojojin da za su bar aikin sojan dai sun fito ne daga sassa daban-daban na rundunoni da bataliyoyi, kuma dukkan su kananan sojoji ne, wadanda yawancin su su ne a sahun gaban yaki a filin daga.
Jami’an sojojin dai sun kunshi ‘Master Warrant Officer daya, Warrant Officers uku, Staff Sergeants 22, Sergeants 29, Kofur 64, Lance Kofur bakwai, da karabitin soja daya.
Dukkan su za su ajiye aiki a cikin watan Mayu, kamar yadda wata takardar sanarwar sojoji ta tabbatar, wadda PREMIUM TIMES ta ga takardar ido-da-ido.
Sannan kuma tuni har Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya sa hannu kan takardar amincewa da ritayar da sojojin su 127 za su yi.
Sai dai kuma jadawalin sunayen sojojin da za su yi ritayar bai tantance adadin wadanda za su yi ritaa don radin kan su ba. Kuma bai fayyace wadanda za su bar aiki saboda lalurar rashin lafiya ba.
Takardar amincewa da ritayar wadda wani Laftanar Janar T.A Gagariga ya sa wa hannu, an umarci dukkan su 127 din kowa ya mika duk wasu kayan sojoji da ke a hannun sa.
“Kamar yadda dokar soja ta sashe na A ya tanadar, ana sanar da ku cewa Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya ya amince da tiyayar da za ku yi, wadda ta kunshi NOW daya da wasu 126.
“Saboda haka sojojin za su tafi dindindin a ranar 26 Ga Afrilu,amma sallama daga aiki kwata-kwata za ta fara daga 26 Ga Mayu.
“Kamar yadda ka’ida ta tanadar, an umarce ni na sanar da dukkan rundunonin da wadannan sojoji ke aiki su kyale domin su je su yi rahoto a Hedikwata tare da takardun su a ranar 5 Ga Janairu, 2021.”
Kakakin Sojojin Najeriya Sagir Musa bai amsa neman karin bayanin da PREMIUM TIMES ta nema a wurin sa ba.
Ajiye kaki da sojoji har 127 za su yi, wadanda dukkan su shekarun ritayar su bai yi ba, kuma wa’adin ajiye aikin su bai yi ba, saboda daewa wurin aiki, ya zo ne daidai lokacin da kasar nan ke fama da matsanancin matsalar tsaro.
Wannan zubar-gaden ritayar kananan sojoji dai ta zo ne bayan wasu da dama sun ajiye kaki cikin watan Yulin 2020.
Sun ajiye aiki daidai lokacin da kasar nan ke gaganiyar yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma ’Yan Bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Dama kuma a baya sojojin sama, na kasa da na ruwa sun koka kan rashin wadatattun sojojin da za a yi yaki da matsalar tsaro da su.
Kwanan nan kuma Ministan Tsaro Basir Magashi, wanda shi ma Manjo Janar ne mai ritaya, ya bayyana cewa sojoji na fama da karancin zarata, kuma akwai karancin kudade a bangaren su wadanda za a ragargaji matsalar tsaro da su.
Sai dai kuma duk da ikirarin Magashi na rashin isassun kudaden yaki da matsalar tsaro, kasafin kudaden da ake bai wa sojoji sun ja makudan kashi daga kasafin kudaden da Najeriya ke yi a kokwace shekara, tsawon shekarun biyar kenan da su ka gabata a jere.