ZIYARAR GUMI DAJIN KIDANDAN: Sama da Fulani 1000 sun ajiye makamai

0

Fulani sama da 1000 ne suka ajiye makamai a lokacin da suke mika wuya da yin alkawarin daina hare-hare da yin garkuwa da mutane ga babban malamin musulunci, Ahmad Gumi a dajin Kidandan, na jihar Kaduna.

A ranar Talata, babban malamin ya kai ziyara dajin Kidandan domin ci gaba da yi a fulani wa’azi da kuma neman a gina musu makarantu da asibitoci a inda suke.

A dalilin wannan ziyara, Kwamandojin Dajin 18 da masu aiki dasu sama da 1000 suka yi alkawarin ajiye makamai.

Wannan ba shi bane karon farko da Gumi ya kai ziyara irin wannan wuri. A watan jiya ma ya kai irin wannan ziyarar Garin Jere, inda ya kutsa can cikin daji domin ganawa da fulani da yi musu wa’azi.

Karanta sanarwar

A yau Talata 19/01/2021 Allah Ya nufi Sheikh Dr. Ahmad Mahmud Gumi shiga dajin Kidandan wanda ya hada Dajin Giwa da Birnin Gwari domin ci gaba kiran Fulani da Assasa gina musu Asibiti da Makaranta da wurin Sana’a.

Sama da kwamandojin Daji (Shugabannin Kidnappers) goma da tawagarsu sama da dubu daya suka yi alkawarin ajiye makamai, tare da fadan wadansu sharudda da wadanda suke basu makamai da kuma dalilan da suke yin wannan mummunan aiki.

Zaman wanda ya samu halartar Shugaban ‘Yan Sandan Jihar Kaduna CP UM Muri da tawagarsa.

Sheikh Dr. Ahmad Gumi da Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam da tawagarsu duk sun sami hallara.

Cikakken video yana nan tafe In Sha Allah.

Share.

game da Author